Main menu

Pages

AMFANIN LEMON - GRASS GUDA SHA DAYA DA YA KAMATA KU SANI 


Amfanin Lemongrass guda sha daya ga (11) Lafiya (Ciyawa-mai-ƙamshin-lemu) 

Lemongrass (Cymbopogon citratus) shuka ce mai daɗin ƙamshi, wato wata irin ciyawace doguwa mai launin kore da ƙamshin lemun-zaƙi. Duk da yake dai bata da alaƙa da lemon-zaƙi, ƙamshin ciyawar mai ƙarfi da ɗanɗano yayi kama dana lemun-zaƙi (amma bata da zaƙi). Ana samun ciyawar a kasashe masu yanayin zafi ko yanayin ɗumi. 

Anfi yawan amfani da ita a ƙasashen Asiya, Afirka da Australia. Haka kuma, anfi yawan amfani da wannan ciyawa a ƙasashen Asiya wajen girki. A ƙasar Indiya kuwa akanyi amfani da ita a matsayin maganin gargajiya (herb). Ana amfani da busasshiyar ciyawar ko ɗanyarta domin amfani na daban-daban. Kuma anfi amfani da ita wajen haɗa shayi , miya ko kori (curry) domin ta zamo mahaɗin kayan ƙamshin girki. Ana samun manta (lemongrass oil) a kasuwa wanda shima ake amfani dashi na daban-daban.


Amfanin da ta keyi sune;

Mai yiwuwa ne kana da wannan shuka a gida ko a lambunka, koma kana amfani da ita, to amma baka san ainahin amfaninta ba ga lafiya, kawai dai ka dauketa shuka ce domin kawai dai gatanan a gida, ko filebo maisa ƙamshi a kofin shayin ka a lokacin da kake kurɓawa. To ka buɗe idanunka, domin kuwa wannan ciyawa amfaninta ya wuce na adon gida kaɗai ko ƙamshin shayinka da kake jin daɗin sha saboda ɗanɗano da ƙamshin da take baka a lokacin da kayi amfani da ita. Ciyawar Lemongrass nada ado da zata iya yima lafiyarka domin inganta ta. Wasu daga cikin amfanin wannan ciyawa mai albarka sun haɗa da:1. Kariya daga ciwon-daji/kansa (Anti-cancer). Shukar lemongrass nada sinadari mai ƙamshi na "citral", wanda binciken kimiyya ya nuna cewa yana kashe ƙwayoyin halitta da ciwon kansa ya harba a jiki (cancer cells). Haka kuma yana inganta lafiyar ƙwayoyin halittar jiki gaba ɗaya (improving cellular health).
2. ƙarin-jini da hana rashin-jini (Anaemia). Lemongrass nada sinadarin "iron" mai yawa, wato sinadari maisa ƙarin-jini domin cikakkiyar lafiya da kuma hana wasu matsalolin rashin jini.
3. Rage hawan-jini (Reducing high blood pressure). Yawan sinadarin "potessium" a cikin lemongrass, sinadarin mai inganta lafiyar zuciya, koda da sauran sassan jiki, na taimakawa wajen hana hawan-jini, cututtukan zuciya, mutuwar sashen jiki, ciwo kansa, matsalolin rashin narkewar abinci da rashin haihuwa, cikin yardar Allah.
4. Kariya da hana girman kananan halittu masu haddasa cututtuka a jiki (Anti-septic) da kuma hana kumburi, wuri yayi ja, da raɗaɗin ciwo a jiki (Anti-imflammatory), musamman taimako ce ga masu ciwon gabobi da sassan jiki da sauransu (gout, arthritis, etc).


5. Yaƙi da cututtukan bakteriya dana fangas (Anti-bacterial and anti-fungal). Don haka, tana maganin zazzaɓin cizon-sauro da taifot (Malaria and typhoid) [yi shayi] , da sauransu. Haka kuma, tana maganin cin-ruwa na yatsun ƙafa da makero [yi amfani da manta] da sauransu ( athlete's foot, ringworm, etc).
6. Maganin mura, zubar hanci da hawaye, ƙaiƙayin ido, atishawa, toshewar hanci (Cold,flue and hay fever).
7. Tace duk wani abu mai guba ga jiki , musamman na abinci, ko wani abu mai cutarwa da fitar dasu daga jiki (Detoxifying). Tana tsaftace hanta, koda, mafitsara da sauransu.
8. Inganta bacci / yaƙar da rashin bacci (Fighting insomnia). lemongrass nada tasiri wajen kwantar da hankali da faɗa da rashin bacci domin samun cikakkiyar lafiya.
9. Taimako ga masu ciwon-suga (Diabetes). Tana rage yawan suga cikin jini, tsarkake saifa da inganta aikinta.
10. Inganta ƙwaƙwalwa (Improving nervous system). Lemongrass na taimakawa ƙwaƙwalwa wajen maida hankali don laƙantar karatu, riƙe karatun da kuma taimakawa wajen sarrafa karatun/ilimi. Sinadarin "magnesium", "phosphorus" da "folate" da ake samu a cikin ciyawar nada tasirin kyautata lafiyar ƙwaƙwalwa.
11. Rage ƙiba (Weight loss). Shan lemongrass musamman a shayi na narkarda kitshe. Tana sanya yin fitsari akai-akai a lokacinda take fitar da duk wani abu mai yawa da jiki baya buƙata wanda zai iya cutar da lafiya.

Da sauransu.

Comments