Main menu

Pages

YANDA ZAKI GYARA GABANKI DA TAZARGADE BAYAN GAMA AL'ADAH

 Yadda Zaki gyara Gabanki da Tazargade bayan gama Al'adah

Uwargida yana dakyau aduk lokacin da kika gama al'ada ki gyara gabanki kuma ki kara tsaftaceshi sosai domin inganta lafiyarki data maigidanki tare da karawa kanki kima agurin maigidan naki. Domin hada wannan magani kina bukatar Abubuwa kamar haka:-1. Sabulun Kuka Ko kuma Ruwan Ganyen Bagaruwa

2. Tazargade 

3. Zuma

4. Farin Almiski

5. AudugaYadda za'ai amfani dasu shine :-

dafarko uwargida zata tafasa wannan tazargade data tanada sai ta tace ruwan tabarshi ya huce sai ta fara wanke gabanta da sabulun kuka ko ruwan bagaruwa. bayan ta gama andauki dan lokaci sai ta kuma wankewa da wannan ruwan tazargade data tace, sai tadauki auduga ta dangwali zuma ta shafe gabanta. sannan sai ta shafa farin miskinta. indai tai haka zata ga abin mamaki da chanji a tare da ita.


Allah yasa mudace

Comments