Main menu

Pages

YANDA ZAKI AMFANI DA HULBA WAJEN GYARAN GASHI, FUSKA DA KIRJI

 Amfanin Hulba ga Mata wajen gyaran Fuska, Gashi da cikowar Kirji.

 A yau inaso in yi wa mata ‘yan uwana karin haske akan hulba, mata dayawa na barnatar da kudi wajen gyaran fatarsu, Karin ni’imar su, gyaran gashinsu da kuma gyaran cikowar kirji.

To yanzu zan fara kawo muku yanda hulba ke gyara fatar jiki.

Gyaran fuska

Zaki samu garin hulba ki dama da madara da zuma ya damu sosai sai ki shafa a fuskar ki, ki barshi kamar minti talatin kafin ki yi wanka, fuskar ki zata yi sheki zai kashe miki pinples ya gyara miki fuska kuma yana maida tsohuwa yarinya.


Gyaran Gashi

Wato shi gashi wani abu ne wanda ke matukar karawa mace kyau da kima shi yasa yake da kyau mu dinga gyara gashin kanmu akai akai wato kuma aduk abun gyara gashi ba kamar hulba, ga masu son gashin su ya yi tsawo da sheki zaki hada garin hulba coconut oil kigauraya sosai sai ki shafa akanki ki barshi yadade akalla kamar, awa daya ko ma fiye da hakan, kuma zaki ringa yin hakan kamar sau biyu a sati guda, sannan zaki kiyi na mako uku, yana kara tsawon gashi, kuma gashin kanki zaiyi kyau da sheki, kuma yana hana karyewar gashi. 

Ga masu amosani, wato dandruff, zaki hada hulba da apple cider ko ruwan khal ki shafa a kanki, da dare ki barshi har gari ya waye, gabaki daya amosani zasu mutu kuma gashin ki zai yi kyau. Gyaran.


 Cikowar Kirji

Babu kamar hulba yana gyara sosai kuma yasa kirjinki ya cicciko ya kara girma da kyau, wasu suna zuba garin hulba cikin abinci kullum sunaci don gyaran kirji in har abun ya zame masu jiki yana gyara sosai, kuma bayan cikar kirji ma yana warkar da cuttutuka da dama a jiki.

Haka kuma ki samun kindirmo mai kyau sai ku hada da hulba kuma sha yana aiki biyu ne farko gyaran kirji na biyu kuma sa ni’ima.

Ga wanda kirjin su ya kwan biyu suna iya hada garin sa da kindirmo, sannan su sami man sa suna shan spoon daya da safe daya da rana daya da marece, bayan haka ma suna iya dafa garinsa su tace su sa tsumma su gasa kirjin su da shi sannan kuma su shafawa kirjin man sa.

Magana ta karshe anan kuma abin fahimta, ba’aso mace mai juna biyu ta sha hulba domin yana kawo nakuda da gaggawa. Na biyu mata masu shayarwa suna iya hada garin hulban a cikin abincin su yana kara nagartaccen ruwan mama, kuma zai sa jinjiri ya kasance cikin koshin lafiya.

Comments