Main menu

Pages

YANDA AKE YIN HADADDEN TSUMIN 'YAR GATA

 Yadda Ake Hada hadin Tsumin 'yar gata

Yadda ake hada shi, za ki samu wadannan kayan kamar haka

-↴ Tsamiya

-↴ Kankara nadi daya

-↴ Minas-nas gwangwani daya

-↴ Dan bashanana gwangwani daya

-↴ Citta dai-dai mizani

-↴ Kanumfari dai-dai mizani

-↴ Masoro dai-dai mizani


Wadannan kayan hadin duk su za ki zuba a tukunya ki zuba ruwa ki dora akan wuta, ruwan dai-dai azanci ki dafa.

Sai ki sauke ki tace, ki rinka sha haka ba sai kinsa sukari ba, za su wanke miki duk dattin mararki ya bude miki kofofin sha'awa zai zamo me alfahari da ita ko da yaushe.
Uwargida kada ki yi kukan cewa mijinki ya mayar da ke bora, ya fi zama a dakin kishiyarki ya fi son ya kusance ta a kan ke, to tafi ki iya gyara domin duk tsoka irin daya ce, wacce ta fi kula da nata da iya gyara shi dole yafi naki ke da ba ki iya gyara shi ba.

To idan har kika iya gyara nan wajen kika kuma iya tarbiyya a gidan mijinki hakika kin sai wa kanki zaman lafiya da jin dadi a gidan mijinki.

Comments