Main menu

Pages

YADDA ZA AMAGANCE CUTAR ULCER DA CUTUTTUKAN CIKIN HANJI

 




Yadda za a hada maganin Cutar Ulcer da matsalolin hanji

Akwai abubuwa da dama a likitancin Musulunci wadanda sukan magance irin wannan ciwon insha Allahu. Kamar yadda bayanai suka gabata. Ga wasu nan kamar haka :





Kayan Hadi:

1. Ka samu Garin Kustul Hindi cokali 7, garin Shammar cokali 7, Garin Habbatus sauda cokali 7, garin Kirfa cokali uku. Ka gaurayasu baki daya acikin zuma mai kyau (Farar saqa).

Zaka rika shan cokali uku safe da rana da yamma har tsawon kwanaki 30.





2. Man Tafarnuwa, Man Habbatus sauda, Man Jirjir, Ka hadasu waje guda. Sannan ka samu shayin Na'a-Na'a mai kyau, Ka rika zuba wancan hadadden man cokali 2 acikinsa kullum da safe ka rika shansa da zuma.





Lokaci

Zaka sha har sati biyar (5 weeks).  in sha Allahu zaka samu waraka daga Matsalar da ta shafi hanji kamar:


- Typhoid Fever (Zazzabin hanji). 

- Ulcers (wato Olsa, gyambon ciki). 

- Indigestion (wato Magwas).

- Appendicitis (Tsakuwar ciki).

- Majinar Qirji, da Majinar ciki.

- Piles (Basur mai sa kumburin ciki, ko kaikayin dubura).






3. Zam - Zam : Kasami Zamzam + Zuma Ka zubata acikin ruwan zam-zam ka rika sha kullum har sati uku.


In sha Allahu zaka samu waraka daga abinda ke damunka ko menene, albarkacin Alqur'ani.


Allah ya sawwake, Allah shi bada lafiya tare da dukkan Musulmai masu jinya.

Comments