Main menu

Pages

TAZARAR DA YA KAMATA A SAMU DAGA YIN BARI ZUWA DAUKAR WANI CIKIN

 



Tazarar da ya kamata Macen da tayi bari ta samu kafin ta dauki wani cikin.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da shawarar cewa akwai bukatar mace ta huta akalla tsawon wata shida kafin ta sake daukar ciki idan ta yi bari. Hakan zai ba ta dama ta warware daga mawuyacin halin da ta shiga.




Sai dai wani sabon bincike na mujallar lafiya ta PLoS Medicine, wada ya yi nazari kan mata masu ciki 72,000, ya bayyana cewa ma'aurata za su iya sake saduwa domin mace ta dauki ciki kuma hakan ba shi da wata matsala.





Gidauniyar Tommy's da ke tallafa wa matan da suka yi bari ta ce matan da suka shirya sake gwada daukar ciki bayan sun yi bari za su iya yin hakan idan babu wasu dalilai na rashin lafiya.




Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana cigaba da gudanar da karin bincike a kan tazarar daukar ciki kuma za ta sanar da mutane idan an samu wani sabon bayani.




Bincike, wanda aka gudanar a Norway tsawon shekaru takwas daga 2008 zuwa 2016, ya gano cewa babu wasu manyan bambance-bambance idan mace ta dauki ciki jim kadan bayan ta yi bari ko kuma idan ta jira tsawon wata shida.





Wannan ya sha bamban da binciken da aka gudanar a Latin Amurka - tare da wasu karin bincike - wadanda su ne suka sa Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da shawarar yin tazarar daukar ciki.




Masanan da suka da suka gudanar da sabon binciken a Norway sun ce akwai bukatar sake nazari kan shawarar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yadda ma'aurata za su iya yanke shawara mai kyau game da lokacin da mace za ta sake daukar ciki.





Shawartar ma'aurata su yi jinkirin wata shida kafin su sake daukar ciki bayan an yi bari ko zubar da ciki abu ne mai tsawo ga wasunsu, musamman idan babu wata shaida a likitance da ta goyi bayan hakan, in ji masanan.

Sun bayar da shawara a gudanar da karin bincike.


Daukar ciki bayan ɓari

Masana sun amince cewa koshin lafiyar mace yana taimaka mata wurin sake daukar ciki da wuri.


An bai wa mata shawara su rika shan kwayar magani ta folic asid a kullum a yayin da suke kokarin daukar ciki har zuwa mako 12 idan sun samu juna-biyu.


Hakan yana rage yiwuwar haihuwar jarirai da nakasa a kwakwalwa da laka.





Kashi 20 cikin dari na mata ne suke fama da barin ciki a rayuwarsu. Sau da dama ba a sanin abin da yake haifar da hakan.

Idan mace ta yi bari akwai yiwuwar idan ta sake daukar ciki ba za ta sake yi ba.




Gidauniyar Tommy's ta ce yana da kyau macen da ta yi bari ta nemi shawarar likta game da ko akwai wasu dalilai da za su sa ki jira na dan wani lokaci kafin ki sake yunkurin daukar wani cikin.





Kazalika ya kamata a yi la'akari da lafiyar tunanin ma'aurata. Wasu daga cikinsu suna bukatar lokaci domin yin nazari kafin su shirya daukar wani cikin.

Comments