Main menu

Pages

TARIN ALFANU DA SIRRIKAN DA KE CIKIN BISHIYAR KANYA

 Sirrika da tarin alfanun da ke cikin bishiyar kanya da magungunan da take Insha Allah

Malaman tarihi suka Ce an yi ruwan dufana babu abinda ruwan bai halakar ba, duk bishiyoyin duniya saida suka mutu banda bishiya daya itace Bishiyar Kanya

Inshaa Allahu duk Ciwon duniya kanya na yi amma Banda mutuwa ko tsufa da yardar Allah!

Ba a sassako Bishiyar kanya kowacce rana Sai ranar da aka haifi Annabi Muhammadu S.A.W. LITININ (MONDAY) Kadai! Banda wannan ranar ba a sassakar kanya Sai wannan rana.


Duk itatuwan duniya babu Bishiyar da ta kai Bishiyar kanya tsufa a duniya Wallahi!
Zan fada muku sirrin Bishiyar kanya amma bazan fadi yadda ake yin maganin H.I.V da Ita ba saboda wasu zasu dinga kasuwanci da shi! Saboda haka bazan fadi yadda za a yi maganin H.I.V da Bishiyar kanya ba amma zan yi bayanin wasu cututtukan Inshaa Allahu.

A sassako 6awon Bishiyar Kanya 6awon za a ganshi baki kuma a bushe, ana iya samunsa da datti, Sai a Dan wanke Sai a shanya ya tsantsame ruwan da aka jika shin, Sai kuma a daka shi Bayan ya bushe, Sai a tankade, in aka tankade ya zama kala biyu kenan;

1-Gari

2-Tsaki

Toh shi tsakin Sai an hada Masa mahadi, shi kuma Garin Daga lokacin ya shiga Aiki Insha aAllahu!

Me Ciwon ciki kowanne iri ne ya Debi garin ya zuba a ruwa ya sha ya warke har Abada Insha aAllahu!

Me fama da Ulcer ya kwaba garin da Zuma Yana sha chokali biyu da safe kafin ya Ci komi, biyu da rana Bayan cin Abinci, biyu da dare lokacin kwanciya tsawon kwana Uku a Jere Inshaa Allahu ka rabu da Ulcer.
Hawan Jini

A nemi Zo6orodo/so6orodo/zo6o/so6o na yakuwa ka jika da ruwa, in ya jiku Sai ka tace ka Debi Kofi daya Sai ka barbada garin kanyar nan rabin chokali, Sai ka sha safe da yamma ka dinga yin haka kwana biyar ajere Inshaa Allahu ka rabu da Hawanjini Har Abada cikin ikon Allah


Cutar Qaba, wadda ta sakko da wadda bata sakko ba

Me fama da qaba ya Debi garin kanya chokali daya, ya matse lemon tsami guda Uku a cikin Zuma daidai misali sai ya rufe shi tun safe Sai dare Sai ya bude ya shanye Inshaa Allahu zaiga Yana fitar da qabar kaman ruwan kabewa a fitsarinsa, ko da ya fitar da ita gaba daya ana son kar ya daina Sai yayi kwana Uku a Jere Yana yi, Bayan nan zai ga fatar marenansa ta yamutse sbd sa6ewar kumburin na Baya, toh Sai ya nemi man Shanu da garin kanyar Sai ya kwa6a ya dinga shafawa a gun kullum da dare in zai kwanta Inshaa Allahu gun zai dawo kamar bai ta6a yin Qaba ba!

Rainin gaba

Nemi ruwa daidai yadda zaka iya shanyewa, sai ka karanta Qulhuwallahu kafa 7 ka tohfa a cikin ruwan, Sai ka Dan Debi garin kanyar nan Sai ka zuba a ciki ka kada Sai ka sha, InshaaAllahu Koda gaban ya mutu ne Baya tashi cikin ikon Ubangiji zai mike!

Ciwon Hakori

A debi garin kanya ya sa a gun Inshaa Allahu zai daina har abada.

Ciwon Kafa

Ya kwa6a Garin kanya da danyan manshanu sannan ya Dan diga kalanzir kadan Sai ya shafe kafar da dare in zai kwanta InshaaAllahu zai warke, haka Ciwon Baya, ko Paralyze a dinga shafawa kwana 7 a Jere InshaaAllahu an warke gabadaya.

Maita/kungiyar asiri/ Muyagu

A nemi kwarya a jika garin kanya chokali Uku a sha ludai daya amma ludayin duma, wallahi duk Wanda ya sha har abada maye ko Dan kungiyar asiri bazai ga kurwarsa ba bare ya kamashi har abada InshaaAllahu!
Cutar Basir: ya dinga zuba garin a ruwa Yana sha safe da yamma kwana Uku an warke gabadaya InshaaAllahu!
Mai Zina: A Nemi allo da tawada a rubuta Ihdinal siratal mustaqeemah kafa daya tak! Sai a wanke da ruwan zam-zam Sai a barbada garin kanya a ciki Sai a bawa Mutum ya sha kuma ya shafa ajikinsa, InshaaAllahu wannan mutumin bazai kara yin ZINA ba wallahi! Kuna iya yiwa yayanku saboda wannan lalataccen Zamani da muke cikinsa, in kuka musu wallahi babu Wanda ya isa yayi zina da Su face mijinsu kadai InshaaAllahu!


Yadda za a yi da tsakin kuma:

A yanko ganyen kuka a daka a tankade Sai a hada tsakin kuka da tsakin kanya a dinga hayaki da shi a Jiki ko a tsakar Gida Yana kone aljanu da Kore mayu. Me fama da farfadiya a Masa alwala a Masa bayanin InshaaAllahu ya daina faduwa, haka me Ciwon Hauka shima a dinga Masa bayanin Bayan yayi alwala Inshaa Allahu zai warke!

Wanda yake tunanin ko akwai sammu jikinsa

A rubuta falaqi da nasi kafa daidai, Sai a sa garin kanya a cikin rubutun Sai a bari Sai dare Sai ya sha ya shafe jikinsa InshaaAllahu take sammun zai kone.

Fitsarin kwance kowane iri ne

A nemi kaikayin gero Sai a jika da ruwa Sai ya kwana Sai a tace Sai a zuba garin kanya chokali guda, duk yawan ruwan kar garin kanyar ya wuce chokali daya, Sai a juye a cikin ruwan a gauraya Sai a bawa Yaro ludayi daya, duk yawan yaran ludai dai dai za a basu kowa, InshaaAllahu har abada sun daina Fitsarin Kwance.

Matsalar Rashin Haihuwa

A samu kwan zabo ko na kazar hausa guda 6, Sai a fasa guda 2 a kada tare da garin kanya Rabin chokali, kuma  a sa gishiri Sai a soya da mai Sai a cinye, haka za a yi ta yi tsawon kwana Uku a Jere kullum kwai shida sun kare kenan, InshaaAllahu kafin watan ya mutu Sai an sami CIKIN, in Namiji ne ke da matsala shi zai Ci, in mace Ce ke da matsalar ita zata ci.


 Nah sadaukar muku da wannan sirri Fisabilillah don Allah Ku yadawa yan Uwa domin mu amfana gabadaya.


Comments