Main menu

Pages

SHARHI AKAN RABE RABEN WASWASI DA HANYOYIN DA ZA A BI DON MAGANCESHI

 




Bayani akan waswasi, rabe rabensa da yadda za a shawo kan matsalar

Waswasi ciwone mai hatsarin gaske, mutane da dama na fama da wanna ciwon. 

Waswasi na shiga ko’ina a cikin rayuwar dan-Adam, kuma yakan jawo kunci, da damuwa ga wanda aka jarabta dashi, an kasa waswasi kashi uku.





 (1): Waswasi a cikin addini. Shine wanda mutum zai dinga jin wasu abubuwa masu nauyin fada ko aikatawa, ko kudurewa.





(2): Waswasi acikin ibada. Wannan na kasancewa wajan tsarki, wajan alwala, wani a wajan sallah, ko Azumi, da sauran ibadu. Yana yi kuma yana maimaitawa, ko yadinga jin sallar bata yiba.






 (3): Waswasi a wajen mu’amala, ya dinga yawan zargin jama’a, da kokwanto, har matarsa yana zargin tana cin amanarsa, ko mijinta tana zarginsa, ko abokansa. ko yadinga ganin kowa makiyinsa ne, baya sonsa da alkhairi sai yawan zargi da kokwanto, da shakka, wani har ta kaishi ga yin kisa.





Abubuwa goma dake maganin waswasi:

1- Neman tsarin Allah 

2- Yawan anbaton Allah

3- Dogaro ga Allah

4- Yawan karatun Alkur’ani da sauraronsa

5- Bin Sunnah da koyarwarta

6- Karanta tarihin magabata

7- Daina yawan zama ba abokin tarayya, da yawan tunanin duniya

8- Yawan Addu’a

9- Abota da mutanan kirki

10- Rashin yarda da duk abinda zuciya ta sakawa mutum. 






Sa’anan mutum Zai lizamci yin wannan addu’a;

1. A’uzubillahi minal shaidani rajim, ammatu billahi wa rusulihi, Allahu ahad, Assamad. Allazi lamyalidi walam yulad, walam yakullahu kufu’an ahad.


2. Radhitu billahi rabbi, wa bil islama dinnan wabi Muhammad (SAW) nabiyan wa rasula. 

Allah ya kara tsaremu da wannan mummunan dabi’a kuma Ya Kara taimakonmu. Amin

Comments