Main menu

Pages

MATAKAI 7 DA ZASU TAIMAKI MACE WAJEN SAMUN CIKI, CIKIN SAUKI

 



Matakai bakwai da shawarwarin da za su taimakawa Mace ta yi saurin daukar ciki

Ma'aurata da dama kan shiga damuwa a duk lokacin da suke kokarin ganin sun samu haihuwa


Babu mamaki akwai tarin tambayoyi a zuciyarki kan yadda zaki dauki ciki, musamman idan kina da larura ko wani ciwo. Kula da lafiyar jiki na cikin matakan farko na iya samun dacewar daukar ciki. Amma kuma me za ki iya yi domin inganta hanyoyin samun haihuwa?





Shawara mafi muhimmanci ga mace da ke son daukar ciki ko samun juna-biyu ita ce sanin yanayin jikinta, musamman lokacin zuwan jinin al'adarta, a cewar Dakta Sajeeda Ibrahim, ƙwararriyar likitar mata a Asibitin Koyarwa na birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.





"Yana da muhimmanci ta san yanayin zuwa da ɗaukewar jininta na haila saboda tsara ko sanin lokutan da idan ta yi jima'i za ta dauki ciki," a cewar Dakta Sajeeda.





BBC ta tattauna da Dakta Sajeeda da kuma Dakta Tanko Zakari, kwararre kan lafiyar mata a Asibitin Mallam Aminu Kano, kan matakai bakwai da za su taimaka wa mace wajen ɗaukar ciki.





1. Bincike domin sanin lafiyar jiki

Kafin ki soma kokarin ɗaukar ciki, ki soma duba lafiyarki. Ki tambayi likitarki domin samun bayanai kan magunguna da ke taimaka wa mace wajen ɗaukar ciki - masu dauke da sinadarin folic asid da ke taimakawa da kuma bayar da kariya kan wasu matsalolin haihuwa da suka hada da haihuwar jarirai masu nakasa.





Sinadarin folic asid na aiki sosai a kwanakin farko na ɗaukar ciki, shi ya sa yake da muhimmanci ki tabbata kina shan sa sosai tun kafin ki yi ciki.




Ki tabbatar kina bin wannan tsari kafin kokarin ɗaukar ciki, a cewar Dakta Sajeeda. "Idan kina da matsala da lalura dole ki nemi magani da daidaita kanki kafin ki samu ciki ba tare da matsala ba."




2. Sanin lokutan haila

Me kika sani game da lokacin zuwa da ɗaukewar hailarki? Fahimtar hakan zai taimaka miki wajen sanin lokacin da ya fi dacewa na daukar ciki a gare ki a cewar, Sajeeda.




Lokacin da mahaifar mace take fitar da kwayaye shi ne mafi dacewa wajen daukar juna-biyu a gare ta.




"Wannan shi ne lokacin da ake son mace ta nuna nacewa wajen jima'i a kai-a kai," a cewar masana.




Hakan na taimakawa wajen gane alamomin fitar kwai, da sauye-sauye da mace ke ji a jikinta da fitar ruwa daga farjinta.




Ruwan na kasancewa fari da ɗan kauri da yauƙi wanda ke isar da sakon cewa shi ne lokacin iya samun juna-biyu. Wasu mata kuma kan yi fama da ciwon mara.






Sannan akwai abin da ake amfani da shi wajen gwada ko mace ta soma fitar da ƙwai wanda shi ma yana taimakawa wajen ankarar da cewa tana cikin lokacin iya ɗaukar ciki, a cewar Dakta Sajeeda.






Ba wai kawai za su tabbatar miki da cewa lokacinki na fitar da kwai ya zagayo ba ne, "idan kina jima'i akai - akai, wannan na sanar da ke lokacin da ya kamata ki sake bayar da karfi domin daukar ciki," a cewarta.




Ga yadda lissafin yake: Ranar farko ta ganin jinin halarki, da ita za ki soma lissafi.




"Ki soma gwaji daga rana ta tara ki kuma ci gaba da hakan har sai gwajin ya tabbatar miki da lissafin.




Mata da ke ganin haila bayan duk kwanaki 28 na iya soma fitar da kwai a rana ta 14.




Sai dai galibin mata yanayin hailarsu na da tsayi wasu kuma gajeren lokaci suke dauka, don haka dole ki natsu wajen tantace lissafinki.




Mece ce makomar masu amfani da magungunan takaita haihuwa? Dole sai kin dan jinkirta kafin ki samu juna-biyu? Likitoci dai na cewa ba lallai ba ne.




"A shekarun baya, wasu bayanai na cewa sai ka ɗan jira na wani ɗan lokaci bayan ka dakatar da shan kwayoyin hana daukar ciki kafin ka shiga fafutikar neman ciki, sai dai wannan karatun a yanzu ya sauya.




Kina iya kokarin ganin kin dauki ciki da zarar kin daina shan magungunan takaita haihuwa," a cewar Dakta Tanko Zakari, kwararren likitan mata a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.




Dakta Tanko ya ce abin da mace ya kamata ta sa a zuciyarta shi ne tana iya daukar ciki kafin zuwan haila, don haka lissafin lokacin fitar kwan haihuwa na iya kasancewa mai wahala, kuma kina iya shan wahala wajen iya gano lokaci ko ranakun da za ki soma fitar da kwan haihuwa.




Bisa wannan dalili, "wasu kan jira har sai zagayowar jinin haila," a cewarsa.





3. Salon kwanciya mafi kyau

Tatsuniyar salon kwanciya mafi dacewa saboda daukar ciki cikin gaggawa, wannan kusan labari ne ko shaci-faɗin mutane.





Bincike ya nuna cewa babu hujja a kimiyyance da ke nuna cewa salon kwanciyar da aka saba - namiji a kan mace- ya fi dacewa da a ce mace ta kasance a saman namiji a lokacin jami'i idan ana kokarin ganin an samu juna-biyu ko neman haihuwa.





"Duk salon kwanciyar da za a yi, indai za a kai ga shiga farjin mace, babu wani bambanci da za a gani ga mai neman haihuwa, a cewar Dakta Tanko.





Sai dai wasu salon jima'i kamar tsayuwa ko zama, na iya hana maniyyi shiga cikin jikin mace.





"Batu ne na son ganin maniyi ya shiga cikin jikin da karfinsa ba za a so ganin bai ratsa wuraren da ake bukata ba, a cewar masana.





4. Kar a tashi da wuri idan an kammala jima'i

Babu mamaki kin taba jin wannan batu -- kwance a kan gado ki ɗaga kafarki sama bayan saduwa domin ƙara damar da kike da ita ta shigar ciki. Mene ne gaskiyar hakan? Zance na zahiri babu gaskiya a wannan batu.





"Yana da kyau ka kwanta a gado na tsawon minti 10 zuwa 15 bayan jami'a, ba kuma lallai sai kin ɗage kafarki sama ba," a cewar Dakta Tanko.




"Kwankwasonki ba ya juyawa idan kin ɗage kafafuwanki sama. "Kuma kar ki shiga bandaki a wannan lokaci, a cewarsa. "Idan kika jira na minti 10 zuwa 15, maniyyin da zai shige ki zai yi aiki yadda ya kamata a mahaifa."





5. Kar ki nuna zaƙewa

Yin jima'i a kullum ko a lokutan fitar kwai ba wai zai kara miki damarmaki ta daukar ciki ba ne.


"Sai dai kawai, a kowanne dare a lokutan fitar kwai da mahaifa ke saki na taimakawa wajen iya daukar juna-biyu," a cewar Dakta Tanko.




Maniyyi na iya zama har na tsawon kwanaki biyar a jikin mace. Shawara mafi dacewa ita ce a rinka yin jima'a akai-akai -- a lokacin da mahaifarki ke sakin kwai, da kuma lokutan da ba kya cikin wannan yanayi.




A kan batun maniyyi, "sanya tufafi mai matse jiki na iya tasiri wajen rage karfin fitar maniyyi yadda ya kamata," a cewar ƙwararru.




Haka kuma daukar tsawon lokaci a cikin ruwan zafi a bandaki ko wajen wankan zamani da ake kira Jacuzzi a Turance. Haka kuma yanayin mu'amala da wayarka ta hannu.




Akwai binciken da ya nuna cewa maza da ke yawan mu'amala da na'urori da ake riƙewa a hannu irin su waya da kuma ajiye su a kan cinya ko kusa da mazakuta na tasiri wajen rage inganci maniyi.




Sannan akwai wani bincike da mujallar kiwon lafiya ta Human Reproduction ta wallafa da ke nuna cewa akwai nau'ukan abinci da ke tasiri ko rage karfin maniyyin maza.


Irin waɗannan abinci sun kunshi abubuwan da ake sarrafawa da waken-soya.





6. Ragewa kai gajiya da samun natsuwa

Ki rage wa kanki tunanin neman 'ya'ya ido rufe. Ki kwantar da hankali ki samu natsuwa, kamar yadda ƙwararru ke bayar da shawara.




Saboda damuwa da jefa kai cikin tunani na iya shafar fitar kwan mace daga mahaifa. Don haka kwantar da hankali da cire damuwa na iya taimaka miki.




Yana da matukar amfani ki rungumi duk wani abu da ke cire miki damuwa, saboda yana da kyau ga lafiyar jikinki.




"Akwai wasu hujjoji da ke nuna cewa ragewa kai damuwa da tarin gajiya na taimakawa wajen samun damar iya daukar ciki, a cewar ƙwararru.




Sannan shan barasa ga mace mai neman ciki yana da matukar matsala wajen samun juna-biyu





7. Kasancewa cikin ƙoshin lafiya

Motsa jiki abu ne mai kyau ga lafiyarki - saboda zai taimaka miki da ƙoshin lafiya da takaita nauyin jiki. Sai dai kuma nuna zaƙewa ko takura kai sama da ƙa'ida na da hadari.




"Motsa jiki da yawa na iya hana mace fitar ƙwai daga mahaifa," a cewar Dakta Sajeeda.




Mene ne yake yin yawa? Abubuwan na iya bambanta tsakanin kowacce mace. Idan kin saba da motsa jiki sosai kuma kina ganin hailarki akai - akai, to salon motsa jikinki ba matsala ba ne a gareki, a cewarta.




Amma Dakta Tanko na cewa, ba ana nufin za a ga daukewar jinin haila ba ne baki daya ga wadanda ke motsa jiki da yawa.




"Abu na farko da ke faruwa shi ne yanayin kidaya salon zuwan hailarki na iya sauyawa.




Ya kamata jinin haila ya zo miki kwanaki 14 bayan fitar ƙwai daga mahaifa, sai dai yawan motsa jiki na iya taƙaita faruwar hakan.




"Wannan na iya kasancewa abu na farko da za a bukaci ki taƙaita wajen cimma burinki.




Ya shawarci bibiyar tsawon lokaci da kike dauka wajen ganin haila bayan fitar ƙwai daga mahaifarki, saboda ita ce hanya mafi dacewa ta tabbatar da yadda kike.




Dakta Tanko na cewa hanya mafi dacewa wajen samun damarmakin ɗaukar juna-biyu, a daidai lokacin da kike samun gajiya ko kula da lafiyarki shi ne takaita motsa jiki - kina iya zaɓin tafiya sannu a hankali na tsawon sa'a biyu da rabi a mako ko na aƙalla minti 30 cikin kwana biyar a sati.




Daina shan barasa ko taba sigari domin samun damar cimma burinki,"in ji Sajeeda.




Baya ga tasirin da shan taba sigari ke yi ga lafiyar jikin dan adam, wannan dabi'a na taƙaita damar daukar ciki. "Tana tasiri sosai ga sinadarin estrogen da fitar ƙwai."




Kuma babu wani abin damuwa kan abubuwan da kike yi a rana. Kashi 85 cikin 100 na matan da suka bi ko rungumi wannan tsari za su iya samun juna-biyu cikin shekara guda, a cewar Dakta Sajeeda


Comments