Main menu

Pages

MAGANIN ZAZZABIN CANJIN LOKACIN NAN DA AKE CIKI

 Maganin Zazzabi na sauyin yanayin nan da ake ciki

Naga mutane nata fama da masassara a wannan lokaci saboda yanayin canjin lokaci da aka samu insha Allah in aka gwada xa a jin dadinshi
Ga Abubuwan da za'a naima Insha Allahu za'a samu waraka.

1. Kimba ta 100 ta Isa


2.Kanunfari 100


3. Ɗanyar citta (Ginger) ta 100
A hada su waje guda a jajjaga su (Blending) sannan a tafasa su a tukunya, idan ya tafasa sai a sauke ayi surace. Amma kafin ayi suracen a ɗebi kofi daya a sha da zafin sa kamar shayi.
A daure a gwada.

Duk wanda yayi haka ba zai kwana da zazzabi ba, Insha Allahu, zaka iya rabawa 2, kayi sau 2.


Allah yaƙara mana lafiya

Comments