Main menu

Pages

KASHE - KASHEN MATSI GUDA UKU YADDA AKE YINSU DA IWADANDA ZASU YI

 
Ire iren matsi guda uku da irin Matan da ya kamata tayi amfani da kowane, ba cushe cushe ba

Akwai kala kalan matsi da ya fi dacewa ace Mace tayi, Matsin nan kuwa kala uku ne gasu kamar haka;
1 - Akwai Matsin da akeyi don farjin Mace ya tsuke ya zama a tsuke, to babu Macen da akeso tayi irin Wannan kalar Matsi sai Macen da gabanta ya bude, ko ta dalilin haihuwa ko kuma wadda akayi ma fyade ta rasa budurcinta, to sai tayi irin Wannan Matsi don ta tsuke.Irin wadannan Mata sune ya kamata suyi Matsin tsuke farji, amma sai kaga budurwa tana tsarki da bagaruwa da kuma Matsi alhalin tana da budurcinta. To yin hakan illane ga 'yammata don haka sai a kiyaye.


2 - Sai Matsi na biyu Kuma ana yinsa ne don qarin dandano da Ni'ima, shi wannan kowace Mace zata iya yinsa har ma da budurwar da ake shirin yi mata aure amma kar ta tura ciki sosai. Sannan akwai sharadin cewa gabanki a tsaftace yake kina yawan tsarki da ruwan dumi, da tsarki da ruwan dumi da Ganyen magarya a duk lokacin da kika gama period.

Sannan ya zamto abinda Zaki saka ya zama yana da inganci ba wai kowane kwashe kwashe da kinji labarin abu sai kawai ki sanya ba. Sannan da zaki dage da tsaftace wajen da ba ruwanki da wani cushe cushe saboda kwayoyin cutar dake shiga cikine ke kashe sinadaran ciki sai Mace ta zama ba taste.
3 - Wannan Kuma shine Matsin da akeyi don magance cututtukan dake gaban Mace, shine irinsu Hulba da ake Zuwa cikin ruwan dumi ana sitbath dashi da sauran ire iren wadannan da Mace zata yi don kiyaye lafiyar gabanta.


A takaice dole idan zakiyi Matsi kisan matsayinsa sannan ne Zaki gane aikin da yayi miki a jiki.


Lokutta da dama Mata kanyi kuskure wajen saka abu a gabansu Wanda Basu san matsayinsa ko ingancinsa ba, wanda shine a qarshe sai kiga ya zama infection.


Allah Ya sa mu gane mu gyara.

Comments