Main menu

Pages

IRE - IREN BASUR YADDA AKE KAMUWA DASU DA YADDA ZA A MAGANCESU

 



Bayani akan Cutar Basir yadda Ake Kamuwa dashi da yadda za a Magance shi

BASIR:- yana samuwa ne a lokacin da jijiyoyin da ke mafitar bahaya suka kumbura daga ciki ko daga waje (wanda muke kira basir mai tsiro), wanda yawancin lokuta hakan na faruwa ne a sakamakon wahala wajen fitar da bahaya.


Basir yafi matsawa wadanda ke da matsalar jinkiri wajen narkewar abinci a ciki, masu ciki da kuma tsofaffi.




Masana kiwon lafiya sun rarraba basir kashi hudu :

1. Jijiyoyin dubura sun kumbura amma bai fara tsiro ba, a wannan lokocin mutum zaina digar da jini kadai ne.


2. A wannan lokocin kumburin na iya fitowa (tsiro) lokoci lokoci, musamman lokocin bahaya kuma da kansa yake komawa.


3. Idan yakai wannan Matakin yana fitowa akai akai kuma baya komawa da kansa sai dai akomar dashi.


4. a wannan matakin yagama fitowa ko tsiro kuma baya komawa ko kakomar da shi bazai zauna ba zai sake fita. 





Abubuwan da ke haifar da Basir : 

1- Yawan zaman waje daya. 

2- Kiba 

3- Juna biyu

4-  Yinkurin haihuwa.

5-  Gudawa mai tsanani

6- Yawan yin kashi mai tauri 

7-  Saduwa ta dubura

8- Daukan abubuwa masu nauyin gaske

9- Yawan zama akan toilet na tsawon lokaci

10- Rashin cin ganye da kayan marmari kamarsu salat da kabeji 




Alamomin Basur

1- Diga ko zubar da jini 

2-  Kumburi ya bayyana daga cikin dubura 

3-  Ciwo sosai amma wasu kan zo ba ciwo

4-  Kaikayi da rashin sukuni .





Abubuwan da zasu taimakawa mai hemorrhoid don samun waraka.:

Wanda ke da basir kaso na daya da na biyu kan iya maganceshi ta hanyar canza salon rayuwa, daina abubuwan da suke kawoshi, amma in har yakai kaso na uku ko na hudu ko yake zubar da jini, wannan aikin sai anje gun likita.





Ga kadan daga cikin hanyoyin da zasu taimaka wajen warkewa :

1- Gaggauta fitar da bahaya a lokacin da aka ji shi ba tare da jinkiri ba.


2- Shan ruwa a kai a kai.


3- Yawaita cin kayan lambu da kayan itatuwa wadanda ke taimakawa wajen narkar da abinci da wuri su kuma sanya bahaya yayi laushi ya fita ba tare da matsala ba.


4- Yawaita motsa jiki da gujewa zama a guri daya na tsahon lokaci.


5- Gujewa zaunawa a yayin fitar da bahaya kamar yadda ake yi a yawancin bandakuna na zamani Zama yana hana ko rage saukin fitar bandaki ya kuma ta’azzara basir. Tsugunne irin na iyaye da kakanni ya fi alkairi


6- Zama a guri mai Laushi a ko da yaushe.


7- sai Neman masana cutar kokuma zuwa asibiti domin baka magunguna da kuma shawarwari.





Illolin Cutar basir

GA kadan daga cikin illar da zai iya kawowa mutum :

1.Daskarewar jini a gun, hakan kan iya sa daskararren jinin yaje ya toshe kanana magudanan jini


2. Rubewar jiki, duk inda baya samun jini a jiki akwai ka'idajjen lokacin da zaikai ya mutu.


3.Yakan sa kwayoyin cutuka su shiga mutun 





SHAWARA

Duk sanda mutum ya tabbata yana da basir yayi kokorin yayi gaggawan zuwa asibiti ko Masana cutar bawai ya tsaya yana saka magungunan gargajiya a duburan sa ba, wanda likitoci sun tabbata yawan saka magunguna da ba kai ba gindi a dubura yana kawo ciwon DAJI (Cancer)


Yana da kyau mutane su kauracewa cusa duk wani maganin asibiti ko na gargajiya a Duburan su .





Maganin basur kowane iri

A nemi Tafarnuwa Manyan Kwallo Guda Uku, Albasa Babba Guda daya, Chitta danya guda uku, Khal Tuffa me hoton Apple Chokali Goma, Ganyen Zogala danye Daidai misali, Zo6o Daidai misali, Garin Goruba Daidai misali, Garin Dabino Daidai misali, Sai a Hadasu da Ruwan zapi Liter daya a Markadesu tare, wato ayi Blending dinsu kenan, me busahshsen bawo a cire 6awon kafin a markada, 





Sai a tace a saka zuma yadda ruwan zai dan yi zaki kadan ba da yawa ba, sai a dinga sha kullum kofi daya da safe in an ci abinci, da rana ma haka, haka za a dinga yi tsawon sati guda, kuma a lokacin da ake wannan treatment din za a dakata da shan siga da duk wani abinci dangin Siga, Kuma a yawaita shan ruwa fiye da dah, Musamman da safe kafin a ci abinci inshaaAllahu indai Basur ne za a warke a rabu da shi, Inkuma Basur Din me tsiro ne toh bayan anyi wannan ga kuma yadda za a magance shi






Maganin basur Mai tsiro

Basir mai tsiro ciwo ne dake da wuyan magancewa da dama cikin mutane suna dauka babu maganinshi har takai sai anje asibiti anyi operation anyanke Wanda yankewar na kashe karfin namiji.


To zamu sanar da maganin shi fisabilillah ga dukkan Wanda yakaranta nauyi ne gare shi ya watsa shi domin amfanuwar al'umma.





Ga duk mai wannan matsalar sai yanemi khal tuffah me hoton Apple sai ya zuba Garin Habbatussauda dan saudiyya a cikinsa, Sai ya dinga wanke duburarsa da wannan ruwan dda kuma Sabulun Salo, Bayan yayi haka Sai ya sami kitsen damo sai a dinga shafawa a wajen tsiron, da yardan Allah za'a rabu dashi kwata-kwata insha Allah.





Kuma wanchan bayanin na sama ba iya me basur bane zai iya amfani da shi no! Duk me bukatar wanke ciki da mara mace ko namiji yaro ko babba budurwa ko me Aure, Me ciki ko marar ciki Zai iya Amfani da shi wajen wanke cikinsa da Marar sa, Yana wanke Jijiyoyin Zakari sosai da sosai, Kuma Yana Sa Karfin Mazakuta, yana kara ruwan Maniyyi, ah! toh Mara ta wanku ciki ya wanku jijiyoyin zakari suma sun wanku ba sai Zakari ya mike ba shima? 




Duk wanda ya sami wannan sako to dan Allah ya watsawa duniya saboda al'ummata karu Saboda Wallahi Basur kullum yana kashe Aure kuma yama sa mata da yawa na cin Amanar Mazajensu suna bin maza masu lafiya a waje suna biya musu Bukatarsu Allah ya kiyaye

Comments