Main menu

Pages

INGANTACCIYAR HANYA DA ZA A BI DON KARYA SIHIRI KOWANE IRI

 Ingantacciyar Hanya da ake karya sihiri cikin yaddar Allah.

Ingantaccen kuma fiyayyen makarin Sihiri shine;

- Ganyen Magarya, 

- Garin hilteet, 

- Man Zaitun da 

- Man habbatus sauda.


Ki samu ganyen magarya guda bakwai, (ko kuma 41 in ji wasu maluman) ki dandaka akan dutse, sannan ki samu ruwa acikin Bokiti ko Kwarya, ko kwano.
Ki zuba wannan dakakken ganyen magaryar acikinsa, sannan ki sanya babban yatsanki acikin ruwan. Ki karanta ayoyin karya sihiri aciki. Kuma kina kusantar da tiririn karatun zuwa kan ruwan.
Idan kin kammala sai ki rika shan ruwan kuma kina wanka dashi awaje mai tsarki.Shi kuma Hilteet ki rika yin hayaki dashi ko  kina sanyawa acikin abincinki. Man Zaitun da man habbah ki karanta ayoyin karya sihiri da ayatush shifa'i acikinsa sannan ki rika shansa kina sanyawa acikin abincinki kuma kina shafawa ajikinki.


In sha Allah sihirin zai karye kuma zaki samu lafiya da izinin Allah.

Comments