Main menu

Pages

HANYOYI HUDU DA ZAKI BI WAJEN SARRAFA GURJI DON GYARAN FUSKA

 



Hanyoyi hudu da za abi don sarrafa gurji(Cocumber) don gyaran Fuska da jiki

1.Ki samu gurji mekyau kiwanke ki mar kadeshi hade da bawon, sannan saiki tace ruwan ki hada da zuma dakuma sabulun wanka na ruwa ki zuba akwalba ko yar roba memurfi ki aje.



Idan kikayi amfani dashi wurin wanke fuska xaibaki kariya ta musanman xaikuma hana fatarki gautsi ko bushewa haka kuma yakan daidaita fitar man fuska ga masu oily skin. Masu dry skin ma zai kawo saukin hakan.




2. Kisami gurji kamar guda uku me kyau wanda bai fara lalacewa ba ki nika a blander. Kitace ruwan saiki hada da ruwan cikin ganyen aloe vera. Kidinga amfani dashi kafin kishiga wanka, ki ajeshi awuri me sanyi ko ki sanyashi a fridge dangudun karyai saurin lalacewa.



Wannan hadine namusanman domin yana sanya fata tayi haske bata kariya na musanman batare da kinyi amfani da mayukan daxasu kona kokuma illata miki fataba.





3. Kishafa xallan ruwan gurji natsawon minti ashirin har xuwa sanda xai bushe sannan kiwanke,yin hakan xai magance fuskarki daga yawan gumi da yawan maiko. Kinga kema saiki shiga jerin isassun mata dan wasu badama sudan shafa hoda tai minti sha biyar saikiga gumi ko maikon fuskar yayi saurin dakushe hasken fuskar. Yakuma ragewa kwalliyar fuskar taki armashi.




4. Ki samu ruwan gurji, zuma, madara, man zaitun.

Kihadasu wuri daya kina shafawa ajikinki da fuskarki. Yana gyara fata hadida sanya fata santsi da laushi. Sannan yakore yan kananan kurajen dakankawowa fuskarki farmaki. Sannan wadda keda dry skin xata sanya farin ruwan kwai acikin hadin. Idan an shafa na dan Wani lokaci sai a shiga wanka

Comments