Main menu

Pages

HANYOYI GOMA SHA BAKWAI DA ZA ABI WAJEN RAGE TEBA DA KIBA

 



Hanyoyi 17 da za a ba don rage teba da kiba ta fuskar Cimaka


Duk wanda yake fama da teba, da kuma to ga hanyoyi goma sha bakwai da zaibi don daidaita yanayin jikinsa ta fannin abincin da mukeci.


1. Ka tabbatar ka karya kumallo a kowacce rana, domin ƙin karin kumallo ba zai taimaka maka wajen rage ƙiba ba, sai dai ma ya hana ka samun kuzari a tsawon ranar da ba ka yi karin kumallon ba.





2. Ka ci abinci na yau da kullum. Domin hakan yana taimakawa wajen ƙone sinadarin (calories) a cikin sauri a lokutan da rana ta take.




3. Ka ci ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki a mafi yawan lokaci, domin ‘ya’yan itace da ganyayyaki suna da ƙarancin sinadarin ƙiba wato (fat).




4. Ka ƙara yawan motsa jiki ko ayyukan da kake yi na yau da kullum.




5. Ka sha ruwa mai yawa, kuma kada ka bar kishirwa a tare da Kai.




6. Ka ci abincin dake ƙunshe da (fiber) mai yawa, hakan zai taimaka maka jin ƙoshin lafiya, da rage maka teba da rage nauyi. Ana samun fiber a cikin abinci da  tsirrai, irin su ‘ya’yan itace da ganyayyaki, hatsi, da shinkafa da taliya, da wake.





7. Ka guji cika cikinka da abinci, a maimakon haka, sai ka rinƙa haƙura da abincin kafin ka ji ka ƙoshi. Domin ciki na ɗaukar kimanin mintuna 20 kafin ya gayawa ƙwaƙwalwa ya ƙoshi.





8. Kada ka haramta wa kanka abincin da kake so, a maimakon haka, kawai sai ka rage yawan cin sa.





9. Ka musanya cin kayan kwalam da maƙulashe ya zuwa cin ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki.



10. Ka guji sha ko cin abin dake da sinadarin giya a ciki.




11. Ka tsara wa kanka lokacin cin abici.




12. Ka hakura da lemukan kwalba da roba.




13. Ka hakura da cika ciki taf kafin ka kwanta bacci. 




14. Kasha Lipton da lemon tsami kafin ka kwanta in baka da ulcer hakan na taimakawa wajen kone kitsen tumbi




15. Rage cin abinci mai sugar sosai hakan na taimakawa wajen rage kiba




16. A samu isasshen bacci saboda sabon bincike ya nuna cewa rashin bacci sosai yakan taimaka wajen kara kiba (nasan wannan zai bada mamaki ga masu karatu)




17. A kwanta a mike sosai a kasa sai a danne kafa ana dagowa ana komawa kullum ana yi ana karawa yana maida tumbi sosai wannan. 

Comments