Main menu

Pages

HADADDEN HADIN KAZAR MAI JEGO, BAYAN ANYI ARBA'IN

 Yadda Ake hadadden Hadin Kazar Mai Jego


Abubuwan da za a nema

- Budurwar kaza ( na gida)


- Saiwar bagaruwa


- Saiwar malmo


- Garin zogale


- Garin biyarana


- Gishirin gallo


- Hakin daka


- Da ruwan kabewa


- Nonon rakumi


Zaki gyara kazar ki cire yan cikin ta sai ki sa saiwowin nan acikin kazar sannan ki dinke ta, ma'ana ki saqa allurai sabbi wadanda zasu riqe wurin, sai ki kifara zuba ruwan kabewa a cikin tukun ya sannan kisa kazar ki zuba gishirin gallon da sauran garukan hadin.ki barshi ya dahu sosai ya kame jikin kazar. Ba a sa komai a haka zaki ci kazar ki shanye romon.......

wannan hadin har ki sake wata haihuwar yana jikinki in shaa Allah zaki sha santi sai yafi na amarcinki yabawa wajen mai gida. Amma se anyi arba'in za a hada aci. Allah bada sa'a

Comments