Main menu

Pages

AMFANIN SINADARIN FOLIC ACID GA MATA MASU CIKI

 Muhimmiyar rawar da sinadaran Folic Acid me takawa ga Mata masu Ciki.

Folic acid Nau’i ne na vitamin B9, kuma yana daya daga cikin vitamin da aka narkar da shi a cikin ruwa (Water-Soluble Vitamins) wanda ake samu a cikin abinci da yawa, mafi mahimmanci daga cikinsu shi ne abinci mai ganye, kuma ana kera shi a matsayin kwaya. 
Kwayar Folic acid ( Folic acid tablets) wasu kwayoyi ne kanana yellow mafi yawa yana zuwa da nauyi 5 (5mg).
Ana amfani da ita wajen magance karancin jajayen kwayoyin jini wanda rashin sinadaran iron yake kawowa.
Wadanda suka kamata suyi amfani da kwayar Folic acid 

1- Mata masu juna biyu

2- Mata masu shayarwa.

3- Masu ciwon hanta.

4- Masu Ciwon Sikila.
Hikimar baiwa Mai Juna biyu maganin Folic Acid

 Folic acid yana daya daga cikin muhimman sinadaran Vitamin da mata masu juna biyu suke bukata, sabida amfanin ta a jikin su.

Ga kadan daga cikin amfanin sinadaran Folic acid a jikin mata masu juna biyu:
Sati ukun farko na dan tayi a ciki , shine lokacin da wasu kwayoyin halittarsa suke haduwa don Samar da ginshiki a kan yadda wasu sassa da kuma tsare-tsaren jikinsa za su kasance,  saboda haka wannan lokaci ne mafi hadari a yadda gabansa za ta kasance ta yadda matsala a haduwar wasu kwayoyin halittar, za su sa ko da ya yi tsawon rai to zai rayu ne da matsala ta har ya mutu. To Folic acid yana taimakawa wajen haduwar wadannan halittun dai dai.
1- Birth defects : Binciken masana ya nuna sinadaran Folic acid yana bada kariya daga haihuwar yaro mai nakasa.2- Folic acid deficiency: Yana kare mata masu juna biyu daga samun karancin sinadaran Folic acid.

Wanda karancin sa zai iya kawo matsalar:


   - Zubewar ciki

   - Naquda kafin lokaci

   - Mutuwar yaro a ciki

   - Mutuwar Uwa.
3- Heart and blood vessel disease : Binciken masana ya nuna sinadaran Folic acid suna taimakawa, wajen daidaita sinadaran homocysteine wanda hakan zai iya bada kariya ga cututtakan zuciya.
4- Cancer: Binciken masana ya nuna sinadaran Folic acid yana iya rage hatsarin kamuwa da ciwon cancer.
5- Depression : Binciken masana ya nuna sinadaran Folic acid yakan iya taimakawa wajen magance matsalar damuwa.
6- Dementia : Hakanan akwai kishin-kishin na yana taimakawa wajen bada kariya daga cutar kwakwalwa wanda yake saka mantuwa.Wasu daga cikin amfanin shan Folic acid

 - Yana Gyara fata

 - Yana Gyara Gashi

 - Yana saka cin Abinci

 - Yana kare matsalolin jijiyoyi.

- Yana taimakawa kula da kyakkyawan ƙwaƙwalwar ajiya.
Idan kinyi amfani da kwayar Folic acid kika ga ya  kawo miki wadannan alamomi maza ki dakatar da ita sannan kije ga Likitan ki.

   - Kaikayin jiki

   - Kurajen Jiki

   - Canza launin fata

   - Rikewar Numfashi
Idan kina amfani da wadannan magunguna kada kisha Folic acid sai kin shawar ci Likitan ki.1- Anticonvulsants: Magungunan jijjiga kaman su  fosphenytoin (Cerebyx), phenytoin (Dilantin, Phenytek), primidone (Mysoline).2- Barbiturates : Magungunan da suke aiki a jijoyoyi wanda suke kai sako ga kwakwalwa. 2- Antimalarial: Magungunan cutar cizon sauro.4- Methotrexate (Trexall): Magungunan da ake amfani da shi domin magance matsalar cancer.
 Kalolin Abincin dake dauke da Folic Acid 

1-  Koren ganye da kayan lambu

2- Nama da Kifi 

3- Wake

4- Hatsi

5- Dawa

5- Brown Shinkafa

 Da sauran su.

Comments