Amfanin Kabewa guda Shida (6) ga Lafiyar Dan Adam
A yau kuma ga mu dauke da amfanin kabewa ga lafiyarmu. Abincinka maganinka. Itama kabewa ALLAH yai mata baiwa da yawa da take taimakawa jikin dan-adam ya samu ingantacciyar lafiya.
Kuma mun san cewa kabewa ba ta da wuyar samu haka nan bata da wuyar sarrafawa, ga kuma ALLAH ya hore mana ita ba ta da wata tsada.
Kamar yadda muka ce ba ta da wuyar sarrafawa, don kuwa ana miyarta, ko a dafa ta, kuma za'a iya soya yayanta ko a bare a ci haka nan.
Yanzu dai ba tare da wani bata lokaci ba ga amfaninta.
1. Gyaran fata.
Saboda baiwar da ALLAH yai mata na gyaran fata har wasu masana na yi mata kirari mai da tsohuwa yarinya. Wannan hadi da zamu bayyana a kasa yana kare fata daga zafin ranar da ke wa fata illa ya sa ta yi sumul abar sha'awa.
Ga yadda abin yake: A samu ruwan kabewa kamar kwatar kofi, danyen kwai guda daya , cokali daya na zuma da cokali daya na madara, a cakuda a shafa, sannan a bar shi tsawon minti 20 a wanke da ruwan dumi. Ki aikata za ki sha mamaki. Ayi haka sau uku duk sati.
2. Taimakawa Masu Ciwon Siga.
Tana taimakawa masu ciwon siga ta wajen rage yawan "glucose" sannan kuma ta kara yawan "insulin" da jiki ke samarwa.
3. Lafiyar Zuciya.
Tana kunshe da wasu sinadarai da ke rage yawan Kwalastaral a jikin dan-adam wanda hakan ke taimakawa zuciya. Amma wannan ya na kunshe ne a yayan na kabewar. Don haka za'a iya bare shi ana ci.
4. Riga-kafin Cutar Daji.
Duk abincin da ya ke dauke da wani sinadari da ake kira da "beta-carotene" na baiwa jiki kariya daga cutar daji. Wannan bayani ya fito ne daga Cibiyar bincike akan cutar daji ta kasar amurka. Kuma an tabbatar da kabewa na kunshe da wannan sanadari mai yawa.
5. Maganin Gajiya.
Sinadaran potassium na taimakawa wajen wartsakewa daga gajiyar da ake fuskanta wajen aikace-aikacen yau da kullum. Ita kuma kabewa na kunshe da wannan sanadarai. Shan kofi daya na dafaffiyar kabewa na sawa a ji garau.
6. Bunkasa Garkuwar Jiki.
Don samun garkuwar jiki mai karfi sai a juri shan kabewa.
Comments
Post a Comment