Main menu

Pages

ABUBUWAN DA MAI CIKI YA KAMATA TAYI, DAGA SAMUN CIKI ZUWA HAIHUWA




Abubuwan da Mai Juna biyu ya kamata tayi tun daga samuwar cikin har Zuwa haihuwa

Daga zarar ciki ya shiga mace za tasamu wasu alamomi da ba ta saba ji ba, (ma'ana alamomin juna biyu kenan). Daga cikin wadannan alamomin akwai :


1- Ketare wata (daukewar jinin al’ada na wata)

2- Tashin zuciya

3- Gajiya

4- Amai

5- Nonuwa suna kara girma.

6- Zazzabin safe

7- Yawan fitsari

8- Yawan kwadayi




Sai dai, wadannan alamomin ba za su tabbatar da cewa mace tana dauke da juna biyu ba, don haka abin da ya kamata ta yi a daidai wannan lokocin shi ne ta yi gwajin fitsari ko jini domin tabbatar da cikin.




Ciki ya kasu gida uku gasu kamar haka:

1- Zango na farko yana farawa daga shigar ciki zuwa watanni uku.


2- Zango na biyu yana farawa daga watanni uku zuwa wata shida.


3- Zango na uku yana farawa daga watanni shidda zuwa haihuwa.





Hanyoyin da Mai ciki ya kamata ta bi don kula da lafiyar ta

1- Idan mace ta yi ciki, yaron da yake cikinta yana zukar jininta saboda shi ne abincinsa wannan dalilin ya sa mata masu ciki suna yawan samun karancin jini .


Yakamata ta samu nau’in abinci mai dauke da sinadarai masu gina jiki, kayan lambu, da kuma kayan marmari kamar su:

Wake, Kifi, Nama, Kwai da sauransu. Sai kuma ganye da kayan itatuwa kamar su :

Salat, Kabeji, Alayyafo, Zogole, Lemu, Kankana, Apple (Tuffa) da sauransu .





Cin abinci lafiyayye yana karawa mata jini , lafiya , yana kara wa yaron da yake ciki lafiya da kaifin basira .




Rayuwar yau da kullum na mai ciki dole ya banbanta da na sauran mutane.

 - Mace mai juna biyu bai kamata ta dinga aikin wahala sosai ba, ya kamata ta dinga hutu ko wacce rana.



 - Idan mace mai ciki ba ta da lafiya dole ta je asibiti domin gudun ka da ta yi amfani da maganin da zai zama mata matsala, ko zai iya kawo matsala ga yaron cikinta .




- Tsaftar muhalli da tsaftar jiki yana da amfani sosai ga mace mai juna biyu domin kare kanta da yaron cikinta daga kamuwa da cututtuka .


-- Macen da take yawan amai ya kamata ta yi amfani da busasshen abinci wanda hakan zai rage yawan amai ko kuma ya tsayar da aman gabaki daya .




 Zuwa awo (Antenatal) yana da amfani sosai wanda alokocin awo za a auna a ga yadda yaro ya kwanta a ciki.

Kuma ana aunawa a ga wasu matsaloli masu kashe uwa da jaririnta domin a magance su , kamar su :


1- Hawan jini

2- Ciwon sugar na masu juna biyu

3- Cutar kanjamau

4- Yawan Jini

5- Zazzabin cizon sauro

6 – Alamar Eclampsia




Muna gargadin mata da su dinga amfani da maganin karin jinin da ake basu a wajen awo (Antenatal).


Mafi yawan mata idan an basu maganin karin jini mai makon su yi amfani da shi kullum, ba sa yi, da sunan wai ba su son warin maganin , wanda wannan baya daya daga cikin dalilin da zai sa a hana mutum shan wannan maganin.




A sani dama can magani ba don dadi ake sha ba, illa dan neman lafiya da neman kariya daga rashin lafiya .




 Sai Kuma daukan allurar tetanus, wannan wata allura ce da ake yi wa mata lokocin awon ciki, amma mafi yawa mata ba sa son wannan allurar saboda rashin sanin amfaninta .

Gaskiya wannan allurar tana da amfani sosai wanda yana daga cikin amfaninta shi ne kare yaro daga kamuwa da wannan cutan mai hatsarin gaske wato (tetanus) .





Motsa jiki lokocin juna biyu na da amafani sosai, ga kadan daga ciki:

- Yana taimako wajen rage ciwon baya, tashin zuciya, kumburin kafa da kuma kunburin Jiki.


- Yana taimakawa wajen kare ko lura da ciwon suga na lokacin goyon ciki


- Yana tamakawa wajen karin karfi


- Yana taimakawa wajen bunkasa yanayi


- Yana taimakon karfin jiki, jinya da kuma lafiyar jiki.


- Yana taimakon ki wajen yin barci mai dadi




Abubuwan da yakamata mace mai ciki ta sani lokacin motsa jiki.


Ta saka kayan da suke matse jiki kamar rigar mama, da kuma daure ciki dan kar a ji ba dadi



Ta kiyaye tsayuwa guri daya lokacin motsa jikin dan kar jini ya taru a kafa.



Ta kiyaye kwanciya a gadon baya, domin ciki yana tare da jijiyoyin na jini zuwa zuciya, hakan yana rage zuwan abinci ga yaron da ke cikin ciki.



Kada mace ta motsa jiki idan tana da wadannan matsalolin:

- Ciwon zuciya:

- Matsalar zubewar ciki

- Rashin lafiyar mahaifa:

-Nakuda kafin lokacin haihuwa:


To Allah Ya sa a amfana, Ya sauki musulmanmu masu juna biyu Lafiya. 


Idan kin karanta ki tura ma wata ta qaru idan kinyi haka kinyi sadaqa

Comments