Main menu

Pages

ABUBUWA GOMA DAKE KAWO CIWON NONO DA YADDA ZA A MAGANCE

 



Cikakken bayanin yadda Ake Kamuwa da ciwon Nono da yadda za a Magance shi

M'anar ciwon Nono shi ne samuwar wasu kwayoyin cuta acikin Nonon mace, wandan da ke haddasa ciwo da canja yanayin nonon mace ko ya lalata shi gaba daya. Ciwon nono wani lokacin yana janyo ru6ewar nono ko yayi sanadin a yanke shi gaba daya.




Yadda Ake Kamuwa da ciwon Nono

Abubuwan da ke kawowa mata ciwon nono sun hada da;


1- Shekaru ko tsufa.

Idan mace shekarunta suka dan fara yawa, to yana da kyau ta fara daukar matakan kariya daga ciwon nono.



2- Sinadarin 'iyistirogen', Idan yay yawa ajikin mace yana haifar da ciwon Nono



3- Fara jinin al'ada; Kafin mace ta kai shekaru sha biyu, za ta iya gamuwa da ciwon nono daga baya.




4-Dadewar Mace tana jinin Al'adah

 Mace ta zarce shekaru hamsin da biyar tana jinin al'ada, shi ma zai iya janyo mata ciwon nono.




5- Rashin haihuwa. Matan da sam ba su haihu ba, har su ka wuce shekaru talatin, za su iya kamuwa da ciwon Nono.



6- Jinkirin haihuwa.

Idan mace ta dauki shekaru da yawa da aure ba ta samu haihuwa ba za ta iya kamuwa da ciwon nono.




7- Girman jiki.

A binciken likitoci, mace mai tsawo da mace mai kiba, sun fi shiga hadarin kamuwa da ciwon nono, musamman masu tarin kitse a jikinsu ko a kugunsu.




8- Gado.

Idan iyayen mace suna fama da ciwon nono, to itama zai iya yiwuwa ta yi gado.




9- Idan Nono daya ya taba ciwo

Idan nonon mace guda daya ya ta6a yin ciwo, to zai iya yiwuwa dayanma ya kama ciwo daga baya.




10- Fitar da tsiro daga Nono

Matar da aka ta6a cire mata tsiro a mamanta, yana da kyau ta dinga zuwa asibiti tana samun shawarwari don gudun kamuwa da ciwon nono daga baya.




Alamomin ciwon Nono sun hada da;

1) Canjin yanayin girman nono.

Haka kawai ki ga nononki yana kara girma ko ya yamutse, ba tare da wani dalili ba.




2) Jin kullutu acikin nono.

Za ki ji kamar wasu abubuwa suna tsirowa daga nononki, har suna kara girma.




3) Canjin kalar fatar nono. Za ki ga fatar nonon tana komawa kamar yalo-yalo ko jaja-jaja ko wata kala daban.



4) Canjin kalar kan Nono (nipples)

Canjin kalar fatar kewayen nono (nipple), ki ga fatar wajen ta yi jajawur.




5) Kumburin kan Nono (nipples)

Kan nonon mace (nipple) ya zama ya kumbura haka kawai kuma yana ciwo.




6) Fitar Ruwa daga kan Nono

Fitar wani ruwa kamar ruwan ciwo haka kawai daga nonon mace. Ba sai lallai matar aure ba, ko da budurwa ce.



7) Radadi da ciwo mai zafi akan nonon da kuma hammata ko da yaushe kuma haka kawai.



8.) Kumburin hammata tsakanin allon kafada zuwa sashin nonon.



9- Jin ciwo mai tsanani idan kika matsa nonon.




Yadda za ki gane kina dauke da cuta a mamanki, tun kafin ya fara ciwo.

1- Za ki ga wani dan tsiro akan nononki amma ba ya ciwo kuma ba ya zafi, wasu matan ma suna dauka kamar wani abin ado ne.



2- Yana iya farawa da jin ciwo kadan a maman.




3- Ya kan iya farawa da ciwo ko kaikayi a fatar da ta zagaye kan nonon.



4- A wasu matan kuma, kan nonon ne yake fara shigewa ciki, za ki ga kan nono daya ya shige ciki, dayan kuma ba haka yake ba. Likitoci suna ganin idan har kan nonon ya lo6a ciki, to cutar ta fara ha6aka kenan.



5- Wasu ya kan fara da fitar wani ciwo a karkashin maman, wanda zai dinga kara yawa, yana kewaye kasan maman kuma ba lallai ne ya zama yana yin zafi ba.




Gargadi da Jan kunne

★ Idan akayi sake ba a dauki mataki da wuri ba, zai iya yiwuwa ciwon yayita ci daga ciki, har ya taso fatar maman, ya zama gyambo wanda yake fitar da jini da ruwa mai wari.




★ Zai iya yiwuwa ciwon nono ya fara ta saman fatar, yana kuma iya farawa daga can cikin nonon, don haka da an ji canji to a gaggauta tuntu6ar masana.




Yadda za a Magance ciwon Nono ta hanyar maganin gargajiya

1- Sakiya. Idan nonon mace ya kumbura har ya ja ruwa, ana iya yin sakiya, wato a yi amfani da kayan aiki wajen huda ruwan ya tsiyaye. Kwararrun masu magunguna ne kadai suke yi. (Sai dai Kuma wannan tsarin na dane, yanzu ba ayi don haka sai a kiyaye)




2- Idan nonon mace yana kaikayi ne, sai a hada Man Zaitun da Man Hulba, ta dinga shafawa.




3- Wacce nonon yake mata ciwo da radadi kuma sai ta samu Garin Ararra6i, ta dinga jika cokali daya, tana sha, kullum, har zuwa kimanin sati daya zuwa biyu.




3- Idan kari ne acikin ciwon, sai a samu Garin Sabara cokali daya, garin Bakin Kajiji rabin cokali, a jika a ruwa, ta sha. Tsallaken kwana daidai, ta sha kamar sau biyar.




Amma dai mafi kyau shi ne aje asibiti ko wajen kwararren mai hada magungunan gargajiya. Allah Ya sa a dace




   


Comments