Main menu

Pages

YANDA ZAKI HADA ANTI - AGING CREAM NA FUSKA DA KANUMFARI

 Yadda Ake hada anti - aging cream na fuska don magance tattarewar fata da yakunewar fuska.A yau mun zo maku da Wani hadi yanda Zaki hada cream da kanki domin keep magance yakunewar fuska da tattarewar fata dake sa a na ganinki kamar wata tsohuwa.
Shi wannan cream zaki dinga shafawa ne a fuska da hannuwa da kafa, da daddare da safe sai ki wanke. Abubuwan da Zaki bukata sune;


- Kanumfari

- Kwakwa

- aloe Vera gel.


Yanda za a hada;

Da farko zaki daka kanumfarinki yayi laushi. Daga nan sai ki samu tukunya ki zuba kanunfari a ciki, sai ki gurza Kwakwa ki sanya kamar cokali daya da rabi zuwa biyu, sai ki zuba Ruwa kamar Kofi daya.

Sai ki barshi ya tafasa sosai zakiga ya koma brown. Sai ki sauke idan ya huce sai ki tace. Idan kin tace sai ki ajiye ruwan gefe daya.
Wannan furkakin da kika tace zaki iya amfani dashi wajen yin scrub, zaki samu zuma rabin cokali ki zuba cikin furkakin sai ki samo almond oil ko zaitun ki zuba cokali daya sai ki scrubbing fuskanki da hannuwanki.
Shi Kuma wancan ruwan da kika tace sai ki dauko aloe Vera gel dinki ki zuba kamar cokali uku, sai ki motse zakiga ya koma kamar cream.
To sai ki dinga shafawa a fuskanki da jikinki kullum kafin ki kwanta, da safe sai ki wanke. Ke da kanki zaki ga yanda jikinki zai kyau ki koma kamar wata sweat 16.

Comments