Main menu

Pages

YANDA WANI MAFUSACIN UBA YA NAKASA JARIRINSA SBD KUKA

 



Yanda wani Uba ya fusata ya nakasa jaririnsa saboda Yana damunsa da kuka

Jami'an tsaro a Najeriya da kungiyoyin kare hakkin bil'adama na neman wani uba da ya karya hannun jaririn sa ɗan wata biyu da gangan saboda yana damunsa da kuka.


Mutumin da aka bayyana sunansa da Mista Confidence Amatobi ɗan asalin jihar Imo a kudancin Najeriya ya tsere tun bayan faruwar lamarin.





Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi kira ga gwamnatin jihar Imo da ta 'yan sanda da su kamo Amatobi, wanda yanzu haka abin da ya aikata ya tilasta yanke hannun jaririn.


Tun bayan faruwar wannan lamari babu wanda ya sake jin duriyar uban jaririn da ya tsere daga unguwarsu bayan ya fahimci girman laifin da ake zarginsa da aikatawa.






Yadda abin ya faru

BBC ta tuntubi rundunar 'yan sandan jihar Imo domin samun karin haske, to sai dai babu wanda ya shigar da kara a gabanta kan abinda aka aikata kan yaron ɗan wata biyu a duniya.


Amma shugabar kungiyar mata 'yan jarida ta Najeriya, NAWOJ, reshen jihar Imo, Dorothy Nnaji ta shaida cewa mutumin ya bugi yaronsa da marikin rataya tufafi, saboda yana damunsa da kuka.





Rahotanni sun ce Mista Confidence Amatobi na da shekaru 31 a duniya. Sannan matarsa, Favor ta na da shekaru 20.


Mahaifiyar yaron Favor, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne tun ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba, 2022 a lokacin da ta miƙa yaron ga mahaifinsa kafin ta fito daga makewayi.





Ta ce ta ji jariri nata yana kuka ba kakkautawa, wani abu da sa ta yi fitowar gaggawa domin sanin abin da ya same shi.


Sai ta gano cewa mijin nata ne ya karya hannun ɗansu kuma cikin karamin lokaci hannunsa ya kumbura. 





Da ta tambayi mahaifin yaron dalilin da ya sa ya karya wa yaron nasa hannu; Amatobi ya ce kukan yaron ne ya dame shi kuma ya hana shi barci da daddare.


Da Amatobi ya ankara hannun dansu ya karye, sai ya ɗaure kafaɗar hannun yaron da sanda da igiya.


A tasa dabaran, sai ya kulle matarsa Misis Favour da jaririn da ɗanta a gidan na tsawon kwana biyu, don kada su samu damar fita da kuma sanar da makwabtansu danyen hukunci da ya aikata kan yaron.






Favor ta ce daga karshe ta samu mafita daga gidan bayan tsawon kwana biyu kasancewar su a tsare.


Bayan ta tsira ne mutanen da take makwabta da su, suka taimaka mata wajen kai yaron asibiti.


To sai dai kaddara ta riga fata wanda bayan karaya a hannun yaro yayi sanadin sai da aka yanke sashen kafadar hannunsa na dama.







Me hukumomin tsaro ke yi a kai?

Tun da farko dai jami’an sintiri sun kama wanda ya aikata laifin wanda ya fito daga karamar hukumar Amurie a Isu ta jihar Imo amma ya tsere.


A yanzu kungiyoyin kare hakkin bil’adama da ke jihar Imo sun sha alwashin zaƙulo wanda ake zargi tare da damka shi a hannun jami’an tsaro domin ya fuskanci shari’a.






Wannan batu ya karaɗe kafofin sada zumunta inda mutane da ke bibiyar shafukan soshiyal midiya ke ta yin tir da mummunan mataki da ya tunzura Mista Confidence karya hannun jaririn da bai wuce watanni biyu da haihuwa ba.


Ko a bara wasu ma'aurata sun kashe ɗan su mai shekara 28 saboda taurin kai a jihar Imo.




Abinda ba a sani ba kawo yanzu shine ko Mista Amotobi ya samu tabin hankali ne ko kuma ya aikata haka da gangan kan kaddarar da ta hau kan ɗan nasu.

Comments