Main menu

Pages

TARIN SUNADARAI DA AMFANIN DANKALIN HAUSA A JIKIN DAN ADAM

 



Amfanin dankalin Hausa a jikin Dan Adam

Kwararru da masana dankalin Hausa sun yi kira ga mutane da su yawaita cin dankalin ganin cewa yana dauke da sinadarorin dake kare mutum daga kamuwa da kowacce irin cuta a jiki.


Dankalin Hausa na dauke da sinadarai kamar haka :

- Calories

- Water

- Protein

- Carbs

- Sugar

- Fiber

- Fat

- Pro-vitamin A

- Vitamin C.

- Potassium

- Manganese

- Vitamin B5

- Vitamin B6

- Vitamin E

- Da sauransu


Wasu daga ciki amfanin da yake yi a jikin mutum sun hada da:

1. Yana kare jiki daga kamuwa da cututtuka.

Dankalin Hausa na dauke da sinadarin Vitamin B6 wanda ke kaifafa kwakwalwa, hana kamuwa da dajin dake kama jini, hana damuwa, kawar da laulayin haila da sauran su.


Dankali na dauke da sinadarin Vitamin C wanda ke warkar da mura, tari, warkar da ciwo ko rauni da sauran su.


Sannan yana dauke da sinadarin Vitamin D dake karfafa aiyukkan hanji, karfafa kasusuwa, hana kamuwa da dajin dake kama fata da sauran su.




2. Yana kara karfin kashi

Dankali na dauke da sinadarin Magnesium da ke taimakawa jikin dan adam wurin hutu inda an gaji kuma yana inganta buguwar zuciya da inganta jijiyoyi da kasusuwan jiki.


Yana kuma dauke da Potassium da ke kawar da cutar koda da kawar da kumburin ciki da taimakawa jiki amfani da sinadaren da ke cikin abinci





3- Yana kara karfin ido

Dankalin hausa na dauke da sinadarin Beta-carotene da jikin dan adam ke sauya ta zuwa Vitamin A da ke inganta lafiyar idanu da karfafa garkuwar jikin dan adam. Karancin Vitamin A a jiki mutum na haifar da wata cutar makanta da ake kira Xerophthalmia.




4. Kara lafiyar kwakwalwa

Cin dankalin hausa musamman mai jan launi yana inganta yadda kwakwalwa ke aiki.


Binciken da masana suka gudanar da dabobi ya nuna cewa sinadarin 'anthocyanins' da jan dankali ke dauke da shi yana inganta lafiyar kwakwalwa da kare shi daga cututuka duk da cewa ba a gudanar da nazirin kan 'yan adam ba.




5. Kawar da cutar daji

Dankalin hausa na dauke da sinadarai masu yaki da kwayoyin cuta 'antioxidant' wanda ke kare jiki daga kamuwa daga cutar daji.




6. Yana Daidai ta Suga

Dankalin Hausa na dauke da sinadaran daidai ta yawan siga a jikin mutum sabida haka yana kawar da cutar siga.

Comments