Main menu

Pages

KWAYOYIN CUTAN DA MACE ZATA IYA KAMUWA BAYAN KARIYAN GABANTA SUN MUTU

 Cututtukan da Mata za su iya fuskanta idan kwayoyin halittansu  suka mutu

Likitoci da dama sun bayyana cewa da zarar kwayoyin halittar da ke kare al'aurar mace sun mutu, to za ta iya fuskantar hadarin kamuwa da cututtuka kamar:
Haifar da kwayoyin cuta (Infection) da za su baibaye al'aurar mace wadanda za su iya kara hadarin jawo nakuda tun lokacin haihuwa bai yi ba, da kuma hadarin saurin kamuwa da cututtuka masu alaka jima'i kamar ciwon sanyi da sauran su.
Yana iya jawo kwayoyin cuta ga mahaifa da kwayayen haihuwa da aka fi sani da Pelvic inflammatory disease (PID). "Wannan al'amari na iya hana mace samun haihuwa kwata-kwata, ko kuma ya sa mace ta dinga daukar ciki a wajen mahaifa," in ji Dakta Hauwa.

Wata mujallar lafiyar mata ta Amurka ta intanet WebMD, ta ce wani bincike da aka yi ya gano cewa mata masu wanke al'aura da sabulu ko sinadarai sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar PID.
Akwai kuma yiwuwar mace ta dinga fama da matsanancin kaikayi a gabanta, ko kuraje su fito mata ko kuma al'aurar ta dinga tsagewa.


A wasu lokutan wani ruwa mai kauri mai kalar dorawa ko kore mai kuma wari zai ta fitowa daga gaban mace, wanda dole sai ta je asibiti don a magance shi.
Ita ma wata kwararriyar likitar matan a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dr Hauwa Umar Shu'aibu, ta ce idan mata suna son su kasance da tsaftatacciyar al'aura, to ya kamata su guji 'cusa abubuwa ko wanke wajen da abubuwa ba tare da shawarar likitoci ba.'


Dr Hauwa Shu'aibu ta ce suna yawan samun irin wadannan matsalolin da dama daga wajen mata."Za ki ga mace ta zo tana korafin cewa tana fama da matsalar kaikayi, ko fitar wani ruwa mai wari daga gabanta, idan ki ka bi diddigin lamarin sosai sai ki samu ko dai yawan wanke wajen da sinadarai masu karfi ne ko kuma cusa wasu abubuwa da nufin inganta rayuwar aurenta.
"A sakamakon haka sai ki ga an shiga wani hali da sai an yi ta neman magani don a samu waraka."
Da yake wannan baiwar Allah ta kawo batun amfani da almiski kuma na san akwai hadisin da ya ce, "Nana Aisha R.A ta kan yi amfani da shi a duk lokacin da ta kamala al'ada," hakan ya sa na bijirowa likitocin wannan tambayar.
Dakta Hauwa Abdullahi da Dakta Hauwa Shu'aibu duk suna kan matsaya daya, inda suka ce lallai amfani da almiskin yana da kyau, amma ba zurara shi za a yi cikin al'aurar ba, abin da ake so mace ta yi shi ne ta shafa a jikin dan kamfai dinta (pant) sannan ta sa pan din.
A cewar su idan aka yi hakan ma ya wadatar, kuma an aikata Sunnar da ake so din.
Al-miski gangariya'

Sai dai shi kansa batun samun almiski gangariya irin wanda Nana Aisha ta yi amfani da shi akwai ayar tambaya a kansa. Wasu na ganin a yanzu ma samun gangariyar almsika 'Musk Aisha' yana da matukar wahala don shi a kan same shi ne daga jikin maƙoƙon Barewa, kuma yana da matuƙar tsada.
Wata mazauniyar Saudiyya, wacce kuma mu'amalarta da Larabawa ya sa ta san kan turarukansu Khadeejah Ummi Madaki ta ce, Musk Aisha na da wahala ake samun sa, don 'yar mitsitsiyar kwalbar ma kan kai riyal 100, kusan naira 10,000 kenan, kuma ba a ko wanne kanti ake samu ba a Saudiyyar ma.
"Gaskiya yawancin almiskin da ake sayarwa a Najeriya ba mai kyau ba ne, gauraye-gauraye ne kawai na turaruka daban-daban, mata kuma sai su saya su yi ta amfani da shi ba tare da la'akari da illar da zai yi musu ba.
"Don haka ya kamata mata su daina bari ana yaudarar su a kawo ko wanne turare a ce Musk Aisha ne," in ji Khadeejah.
Matakan da za a bi wajen tsaftace al'aura

Daga Dr Hauwa Isa Abdullah da Dr Hauwa Umar Shu'aibu


Tsarki da ruwa kawai ba sabulu. Amma Dr Hauwa Isa Abdullahi ta ce, "Kina iya amfani da sabulu kamar na jarirai ki wanke al'aurar sau daya a wata, wato kamar lokacin da ki ka kammala al'ada."Idan kina son tsane wajen bayan kin yi tsarki to kar ki yi hakan da toli-fefe, (toilet paper), zai fi kyau ki tanadi kyalle mai tsafta ki goge da shi.Dr Hauwa Isa ta ce, "Amfani da toli-fefar ba shi da kyau don za ta iya murmushewa ta shige cikin al'aura kuma hakan zai iya sa wa mace kwayoyin cuta. Sannan kuma barin wajen da danshi ma yana iya jawo yaduwar kwayoyin cuta (bacteria).Ka da ki dinga cusa magungunan mata ko turare a al'aurar, idan ma almiskin ne zai fi kyau ki shafa a dan kamfanki kawai.

Ka da ki dinga zama a cikin ruwan dumi da dettol, zai fi kyau ki dinga zuba gishiri a ruwan dumin idan ma kina son zama a ciki ne maimakon dettol. Dr Hauwa Shu'aibu ta ce, "Dettol yana da karfi sosai zai iya kashe kwayoyin halittar da ke al'aurar wadanda suke kare ta daga kamuwa da cututtuka."Yawan sa dan kamfai (pant) yana da muhimmanci, ka da a dinga zama ba pant.

Idan kin wanke pant dinki to zai fi kyau ki shanya shi a rana, "Hasken ranar yana taimakawa wajen kashe kwayoyin cuta idan har akwai a jikin pant din, shanyawa a bandaki ba shi da amfani," in ji Dr Hauwa Shu'aibu.
- Yana da kyau bayan pant din ya bushe idan da hali a goge da dutsen guga (Iron).


- Ki guji sa pant idan bai karasa bushewa ba.


- Idan kina tsarkin bayan-gari to ki fara gogewa tukunna, sannan sai ki wanke amma ki guji ruwan tsarkin ya taba al'aurarki.


- Ki dinga amfani da pant mai taushi ba mai santsi ba.


- Ki yawaita tsarki da ruwan dumi.

Comments