Main menu

Pages

KO KUNSAN RIKE FITSARI YANA HAIFAR DA ILLOLI HAR GUDA TAKWAS

 



Illoli guda takwas da riqe fitsari ke haifarwa, da dabi'n dake kawma kidney matsala

Yau mun kawo maku abubuwa guda takwas da illar rike fitsari ke kawowa, da Kuma abubuwan dake haifar ma Koda(Kidney) matsala.

1. Kidney Stone: rike fitsari a mara ya na haifar da cutar koda da ake kira ‘kidney stone’ a turance.




2.  Damage to pelvic floor muscles: ya kan rage karfin bangaren jikin da yake hana fitsari fita a kowani lokaci wanda ake kira da ‘Pelvic Floor muscles’. Idan wannan guri ba shi da karfin, mutum zai dinga digar da fitsari a koda yaushe.





3- Bladder stretching: ya kan sa mafitsara (bladder) ta girma kamar balam balam waanda hakan zai aifar da mutum yana jin fitsari ammaa idan yaje ya zauna fitsari baya fita.

 




4- Urinary Tract Infection : yakan kawo bawa kwayar cuta Daman zama a mafitsara Wanda yakan zuwa da alamomi kamar haka Ciwon mara, zafi lokocin fitsari, rashin samun fitsari sosai.





5- Interstial bladder: yakan kawo matsalar ciwon mafitsara mai sanani wanda yakw zuwa da takura idan an zauna fitsari.




6- Kidney damage : idan fitsari ta cika mafitsara zaibi hanyar ta koma kidney wanda hakan zai lalata kidney gabaki daya.




7- Incontinence : yakan iya kawo matsalar yoyon fitsari lokocin da mutum yana dariya ko tari.




8- Urine retention: zai sa hanyar fitsari ta toshe hakan ta hana fitsari fita gaba Daya , kafin fitsari tafita sai ansawa mutum hanyar fitsari na roba.




Wasu dabi'u dake kawo ma Koda (Kidney) matsala

Matsalar koda (Kidney) tayi yawa a kasar mu Najeriya to ga kadan daga cikin halayyar mu da take kawo matsalar:

1- Rashin shan isheshshen ruwa.

2- Rike fitsari a mafitsara sai ya takura maka.

3- Amfani da manda/gishiri diyawa.

4- Yawan amfani da magungunan dauke ciwo.

5- Yawan cin abinci masu gina jiki (proteins).

6- Yawan shan barasa (giya).

7- Yawan amfani da sinadaran caffeine. 

8- Sai kuma rashin isheshahen bacci.

Comments