Main menu

Pages

HANYOYI NA MUSAMMAN DA ZA A SARRAFA DABINO DOMIN SAMUN NI'IMA

   Hanyoyi na musamman da za a bi domin sarrafa Dabino don samun Ni'ima.  

A kimiyance shi dabino yana da tarin sinadarai da jiki ke bukata. Kusan vtimins irin vitamin A Calcium iron menerals B complex da irinsu amino acid duk ya tarasu. Shi kansa dabino ruwan cikinsa yafi aiki shi yasa nake son koya maku ynda zaku ribaci ruwan dabinon ku ma aurata da masu shirin auren. Amman banda marasa aure
Taya za a sarrafa dabino domin samun niima?

Zaki samu abubuwa kmr haka. Garin minannas, madarar ruwa sai dabino.

Da farko zaki samu dabino: Ki bare dabinonki rabin kwano, ko dai wani adadi me yawa haka. sai ki jika da ruwa Idan ya yi luguf sai ki markada a ‘blander’ Zaki ganshi da kauri kirtif. Sai ki ajiye a frigde
 Ko wani wuri me sanyi wanda ba zai lalace ba. duk sanda za ki sha saiki debi cokali biyu ki zuba a kofi, ki juye madarar ruwa gwangwani daya, ki sa garin minannas karamin cokali ki juya sosai, Idan ya yi kauri da yawa ki kara ruwa kadan ki kuma juyawa, ki shanye duka. Bayan awa uku da shan ki za ki ji sauti sosai a tare dake. Uwargida da Amarya sai a gwada.

Comments