Main menu

Pages

JARUMA 'YAR TIKTOK MURJA TA FASHE DA KUKA SBD SHARRIN DA AKAI MATA

 Jaruma Kuma 'yar TikTok Murja Ibrahim ta fashe da kuka saboda K'azafin da akai mata.

Abin ban tausayi, Murja Ibrahim Kunya ta fito tana kuka da idonta akan bibiyar ta da ake da sharri. Tayi bayanin abubuwan da tasan tayi har akace an kaita kotu.
Tace ita dai ta san tayi zage -zage sau biyu da lokacin da aka nuna videon wadanda aka sace na cikin jirgin kasan Abuja - Kaduna, da Kuma wani da yayi mata maganar tana da bille, sannan tace har gobe ba tayi dana sanin zage -zage da tayi ba.
Sannan ta kara da cewa akwai fa masu laifi da yawa a social media gasu nan ana ganinsu sai ita, to tasan Wanda yayi mata wannan cinne, tunda babu wanda ya kawo mata takardar sammaci. Da sauran bayanan da tayi. 

Ku Kalli video kuji cikakken bayanin da tayi. 

Comments