Main menu

Pages

YADDA AKE HADA MUHIMMAN SABULUN GYARAN FUSKA, DILKA DSS

Yadda Ake Hada Sabulun na Musamman Domin Gyaran Fata Da Gyaran Fuska Da Kuma Hadin Dilka. 


Assalamu alaikum Warahmatullah

A yau mun zo maku da muhimman abubuwa wato yadda Ake Hada Sabulun fuska da yadda Ake Hada Dilka.


1) Domin Gyaran Fuska

     Za a samu samu:-

1 . Garin zogale

2 . Farar albasa

3 .Sabulun ghana 

4 . Sabulun Dettol

5 . Sabulun salo


Yadda za a hada. 

Ki samu sabulun ghana dana salo dai dai kai daya sai ki samu dettol shima kamar guda 2 sannan sai ki sami garin zogale cokali 2 sai albasa manya guda 2 duk sai ki hada su a turmi ki kirbe su sannan sai ki juye a roba mai murfi zaki dunga wanke fuskarki da shi yanada kyau sosai yana magance kurajen fuska. 2) Hadin Dilka

1 . Dilka da sukari

2 . Lemon tsami

3 . Man zogale

4 . Turaren Du'aul jannah 


   Yadda za a hada:-

Zaki zuba duk kayan a cikin ruwa sai ki sa wuta amma kadan har sai ya tafasa yayi kumfa sai ki sauke idan ya huce kirinka dangwala kina shafawa a ko ina a jikinki, ki bari ya bushe, zai fara murmushewa da kansa sai ki karasa murje shi sai kiyi wanka da ruwan dumi, fatarki zatayi kyau


3) Hadin Sabulu na Musamman

  A samu:-

1 . Madarar turari

2 . Lalle da dilka 

3 . Ganyen magarya

4 . Kur kur 

5 . Dudu osun da Detol

6 . Sabulun ghana


a hadasu wuri daya a daka su a turmi mai kyau su hade jiki sosai sai ki ringa wanka da shi. 

Comments