Main menu

Pages

TARIN AMFANIN YA'YAN ADUWA ( DESERT DATES ) A JIKIN DAN-ADAM.

 Amfanin Aduwa ga Lafiyar Dan Adam

Ana amfani da ita a al'adance don magance cututtuka daban-daban wato kamar ciwon hanji, raunuka, zazzabin cizon sauro, syphilis, farfadiya, ciwon ciki, Ulcer, gudawa, basur, ciwon ciki, asma, da zazzabi. Ya ƙunshi furotin, lipid, carbohydrate, alkaloid, saponin, flavonoid, da Organic acid.


Aduwa na daya daga cikin nau'ukan tsirrai da ke da matukar amfani amma ba a ba ta muhimmanci ba saboda rashin sanin amfanin nata.


Bincike ya nuna cewa aduwa ta samo asali ne daga kasashen yankin Sahara da kuma kudancin Asia.


Ana samunta a Indiya musamman a Rajasthan, Gujarat Madhya Pradesh da Deccan.


A Afirka, tana daya daga cikin itatuwan da aka fi amfani da su a kasar Senegal, kuma tana iya jure wa nau'in kasa iri-iri - mai nauyi da maras nauyi.


Cibiyar tattara bayanai kan hallitu ta duniya (NCBI) ta bayyana cewa ganyen aduwa na dauke da sinadarin saponin, da furanocourmarin, da flavonoid, da glocoside da kuma diglocoside.


Wani abin mamaki game da aduwa shi ne komai nata yana da matukar amfani ga jikin dan adam - kama daga ganyenta har saiwarta .Amfanin aduwa ga lafiyar dan adam.

Da yawa mutane ba sa kallon aduwa a matsayi wani abu mai muhimmanci duba da yadda aka fi samunta a makabarta ko dazuka.


Kamar yadda cibiyar tattara bayanai kan halittu ta duniya ta wallafa, binciken masana da dama ya nuna cewa aduwa na da matukar amfani ga lafiyar bil'adama.

An yi nazari kan amfanin aduwa ga lafiyar jikin dan adam na farko:Magance matsalar sinadarin acid a ciki

Idan mutum ya zamana cewa sindarin acid dayake cikin sa ya yi yawa, wanda hakan zai haifarwa da mutum kumburin ciki, da gyatsa wani abu da ka iya takurawa lafiyar dan adam ya hana shi sukuni.


Kamar yadda mujallar health benefit times ta rawaito shan yayan aduwa yana matukar kawo saukin wannan matsalar ganin cewa yayan itacen na kunshe da sindarin saponosis.Magance matsalar ciwon kafa.

idan aka jika saiwar aduwa aka bawa mai matsalar kafa wanda ko tashi baya iyayi to lallai zai samu sauki daga radadin ciwon kafar, dama samun damar sake takawa.Magani ga masu jego

Wasu suna ganin lallai idan mata basu yi wankan jego ba to lallai akwai matsaloli da zasu biyo baya to amma duk aduwa tana taimakawa wajen kare mata daga wadannan matsaloli in anyi amfani da ita yadda ya kamata.


Mata na amfani da saiwar aduwa wajen wankan jego, abinda ke saukaka wankan ga masu jego.


Idan mace tayi amfani da saiwar aduwa bayan haihuwa bazata samu wata matsala ba da ta danganci ta jego.Kara kaifin basira

Duba da yanayin zaki da aduwa take yadda kwallon aduwar yake kara kaifin basira ga mutane musamman yara kanana.Maganin cutar cizon sauro (malaria).

Malaria dai cuta ce da ta addabi mutane musamman a kasashen Afirka.

shan ruwan tafashen ganyen aduwa yana maganin cutar cizon sauro.Kare garkuwar jikin dan adam

Kamar yadda cibiyar tattara bayanai kan hallitu ta duniya (NCBI) ta wallafa a shafinta na intanet, sinadaran flavonoids da phenolics da ke cikin aduwa na ba da kariya daga yaduwar kwayoyin halitta da ke haddasa cutar kansa.


Har da ma wasu cututtukan da kwayar cutar bacteria ke haddasawa a jikin dan adam tare da kara inganta lafiyar jikin.Maganin asma

Ana nika aduwa sai adinga amfani da garin ana tafasawa a sha , to lallai mai ciwon asma zai samu sauki.Maganin 'Aljanu'

Ganyen aduwa ya na maganin korar shedanu daga jikin dan adam. Ana samo ganyen haduwa hade da kayoyin dake jikin icen aduwar a busar dashi sai a dake ya zama gari domin yin turaren konawa da shi.Daidaita bugun zuciya

Mutane da ke fama da yawan bugun zuciya wanda yake sasu zama suna cikin wani yanayi na razana a koda yaushe , kokuma numfashi ya masa wahala sakamakon bugun zuciyar yayi kadan.


Shan aduwa hakan nan yana taimakawa wajen daidaita bugun zuciyar.

 

Ciwon Ulcer ( Gyambon Ciki ) 

Shan Ya'yan Aduwa Da Bai Wuce Guda 9 Ba A Rana Yana Maganin Ulcer. Gyaran fata

Ana iya amfani da man aduwa wajen gyaran fata. Shafa man aduwa ga fata yana sa tayi sheki da laushi.


Ciwon Suga 

Shan Ya'yan Aduwa Yana Daidaita Sukarin Dake Jinin Mutum.

Comments