Main menu

Pages

LALLAI AKWAI CAKWAKIYA, TALLAR SHIRIN LABARINA

 Akwai cakwakiya a Shirin Labarina Season 5


Assalamu alaikum Warahmatullah

Lallai kam Shirin Labarina season 5 ya zo da sabon salo, ya Kuma zo da cakwakiya da gar gitsi da harigido. Wannan post mun kawo maku short video ne akan tallar Shirin Labarina Season 5.
Cikin satin nan ne mukai sanarwar cewa Shirin Labarina zai zo maku a Litinin din da ta gabata 15 ga watan nan da muke ciki. To ashe munyi misunderstanding akan bayanin da Director Aminu Saira yayi, inda yace za a saki tallar Shirin ranar Litinin.
Mu kum a sai bamu fahimci sakon ba muka sauka ranar Litinin din ne za a saki. To a yanzu dai sun saki tallar kamar yadda sukai alkawari, sannan sun sanar da ranar da lokutan da zasu ringa sakin Shirin da Kuma inda za aringa haskawa.
Sun sanar a rubuce a karshen tallar cewa ranar 2 ga watan September zasu saki film din, a YouTube da misalin karfe 8:30 na dare, sai Kuma da karfe 9;00 na dare a haska a tashar Arewa 24.
Don haka sai ku tara ranar Juma'a 2/9/2022 da misalin karfe Takwas da rabi da Kuma Tara na dare. Sai a yafemu a bisa kuskuren fahimta da muka sanar.

Ga video tallar Shirin ku gani, zaku San 
cewa akwai Qura kwance a cikin Shirin.


Comments