Main menu

Pages

KIRA DA KIRARIN DA QABARI KE YI A LOKACIN RUFE MAMACI

 


Ire - iren Kira da kirarin da qabari ke yi a lokacin da aka zo binne mamaci

Wata rana Manzon Allah (saww) ya shigo Masallacinsa sai ya tarar da wasu Mutane suna ta zance suna dariya.


Sai yace musu: "Amma da ace kuna tunowa da Mai yanke jin dadi (Mutuwa) da wannan ya shagaltar daku daga wannan abinda nake gani.


Ku yawaita Ambaton mutuwa domin wallahi babu wata rana da zata wuce fache sai QABARI (yayi ma kansa kirari) yana cewa:


"NINE GIDAN BAQUNTAKA! NINE GIDAN KADAITAKA!! NINE GIDAN TURBAYA!! KUMA NINE GIDAN TSUTSOTSI!!"


Idan aka zo binne Mumini acikin Qabarinsa, sai Qabarin yace masa:


"MARHABAN WA AHLAN.. WALLAHI KA KASANCE DAGA CIKIN MAFI SOYUWAR MUTANE AGARENI ACIKIN MASU TAFIYA ADORON QASA..


YANZU IDAN AN BINNEKA ACIKINA, NINE SUTURARKA NI ZAN AIKATA MAKA SAKAMAKON IRIN ABINDA KA KASANCE KANA AIKATAWA NE".


Nan take za'a fadada masa Qabarinsa har iyakar ganinsa, Kuma za'a bude masa Qofa zuwa gidansa na Aljannah.


Amma idan akazo za'a binne Kafiri ko Fajiri (Mai aikata manyan laifuka) Sai Qabarinsa yace masa:


"BA'A MARABA DAKAI, KUMA BA'A MURNA DA ZUWANKA.


KUMA WALLAHI KANA DAGA CIKIN MUTANEN DA NAFI QINSU DAGA MASU TAFIYA ADORIN QASA.


YAU ZA'A BINNEKA ACIKINA, NINE SUTURARKA, KUMA ZAN AIKATA MAKA SAKAMAKON IRIN AYYUKAN DAKA KASANCE KANA AIKATAWA".


Nan take sai Qabarin ya matseshi, har sai Qasusuwan hakarkarinsa sun shige cikin junansu.


(Sai Manzon Allah ya sanya yatsunsa cikin junansu -abisa misali).


Sannan za'a turo masa wasu Manyan MACIZAI GUDA SABA'IN (MASU MIYAGUN KAMANNI). 


DA ACE 'DAYAN CIKINSU ZAI HURA QASAR DUNIYAR NAN DA BAKINSA, DA HAR ABADA DUNIYAR NAN BA ZATA TA'BA TSIRO DA CIYAWA BA.


ZASU YI TA SARANSA, SUNA CIZONSA HAR ZUWA LOKACIN DA ZA'A TAFI FILIN HISABI."


- Imam Tirmizy ne ya fitar da Hadisin. sannan Ibnul Jawzy ma ya kawoshi acikin babi na biyu acikin littafinsa mai suna AHWALUL QUBOUR.


Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!

Comments