Main menu

Pages

TA RASU SAURA KWANA 15 BIKINTA
Amarya ta rasu sati biyu kafin bikinta

Allah Sarki, rayuwa a kullum Bawa da buri yake mutuwa. Sannan a kullum Muna cikin tsara rayuwa da shimfida tabarma don gyara zama cikin Duniya bamu sani ba Ashe ajalinmu na kusa.Kamar yadda wannan Amarya itama Allah Ya karbi rants kwanaki shabiyar kacal ya rage ta amarce da angonta. Allah Ya rigada Ya kaddara ba zata taba yin rayuwar aure a Duniya ba.Ta Rasu Saura Kwanaki Goma Sha Biyar Ɗaurin Aurenta Kamar Yadda Rahotanni Suka Baiyana.Allah ya yiwa Rukayya Ibrahim Toro rasuwa a jihar Bauchi, Rukayya ta rasu yau, inda ya rage saura kwanaki 15 ɗaurin Aurenta.


Anan Muke Addu’r Ubangiji Allah ya jiƙanta Ya Gafarta Mata Da Rahama Mukuma Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani Amin

Comments