Main menu

Pages

CIKAKKEN BAYANI YADDA AKE GANE FAKE ALERT NA BANK TRANSFER

 



Yadda zaku gane fake alert na bank

Assalamu alaikum Warahmatullah

A yau nazo muku da bayani akan yadda zaku gane fake alert wato sakon turo kudi na banki.


Kamar dai yadda kuka sani a yanzu muna cikin wani yanayi, wanda kusan kowa yana bukatar tallafi, sannan kuma muna cikin gwamnatin da take yawan bude shafuka domin cike tallafi wanda za a tallafawa matasa da kudi domin dogaro da kansu.



Wannan abubuwan dana lissafo sune suke kusan haddasa ire iren fake alert da yake faruwa har mukan kasa gane alert na kwarai, kasancewar ana yawan cike ciken tallafi kowa yana jiran yaji an turo masa kudi, shiyasa ake samun bata gari su aikawa mutane sako na fake alert domin su samu damar da zasu yaudare ka.



Dan haka ga yadda ake gane fake alert.

Da farko idan har kaga an turo maka sako na kudi, abun daya kamata ka fara dubawa domin gudun fake alert shine, email address dinka idan har already kayi Link dinsa da bank din naka, idan sakon da aka turo maka na gaskiya ne, tabbas za a turo maka irin sakon a email din naka, idan kuma kaga an turo maka sakon kudi kuma ba, a turo maka ta email ba, kuma ka hade email din da bank, to akwai yiwuwar fake alert ne.



Duba Balance: Don gane fake alert yana da kyau idan an turo maka kudi ka duba balance dinka domin tabbatar da kudin, sannan kuma ajikin sakon shima ka duba, zakaga sakon yana dauke da asalin balance dinsa, idan kaga sabanin haka to fake alert ne.



A sakon fake alert ka lura dakyau wasu suna turo sakon hade da wani link wanda zasu umarci daka shiga link din, to ka kiyaye muddin kaga sako yana dauke da irin wannan link fake alert ne.



Duba daga inda aka turo sakon: ka lura dakyau idan aka turo naka sako ka duba daga ina aka turo sakon domin wani lokacin idan ka lura zakaga daga number waya aka turo sakon, amma kasancewar kaga sakon kudi, baka lura da inda sakon ya fito ba, kaide burinka kudine, dan haka ka lura irin wannan shima fake alert ne.



Idan sako yazo daga banki ko kamfani zakaga baya dauke da wajen yin reply na sakon saide kaga Sender does not support replies, wato bazaka samu damar yin reply ba, dan haka sai a kula idan an turo sako daga banki zakaga babu wajen yin reply.



Duk da wasu masu turo sakon fake alert suna amfani da wasu hanyoyin wanda idan sun turo sakon zai nuna musu Sender does not support replies, kamar yadda na gasken yake. amma duk da hakan sai a kula dakyau.

Comments