Main menu

Pages

SUBHANALLAH, MUGUN ALKABA'I DA BITA DA KULKIN DA AKAI MA UMMY RAHAB BAYAN AUREN TA  Mugun Alkaba'i da mugun fatan da akai ma Amarya Ummy Rahab


Mutane da yawansu hassada da bakin ciki da fatan sharti ga 'yan uwansu Musuiyayi masu katutu a zuci, shiyasa sai ayita Shan wahalar rayuwa ba a cigaba saboda mugun nufin da muke yima Yan uwa Musulmai.


Annabi Muhammad SAW yace idan zakai magana idan ba Alkhairi zaka fada ba to kayi shiru da bakinka shine cikar Imaninka. Sannan Imanin dayanku baya cika har sai ka so ma Dan uwanka abinda kaso akan kanka. A Wani Hadisin kenan, to Amma yanzu rayuwar wasu Musulma sunayi ne kawai basa tuna su din suwaye basa tuna dokokin addini duk lokacin da suka tashi yin Abu kawai sai su bi son zuciya da hassada da ganin kyashi.Kwana biyu kenan yau da Ummy Rahab ta shiga dakin mijinta, Wanda Muna mata fatan Alkhairi da cewa wannan aure an daura shi kenan ba maganar rabuwa Insha Allah sai mutuwa.


To sai ga wani can Wanda bai San ciwon kansa ba ya fito tun ajiya yana Mata mugun fata saboda tsananin rashin sanin ciwon Kai da yin abinda ya kamata, yazo Yana fadin maganganun da Basu dace ba a game da auren na Ummy Rahab.

 Ga Video ku kalla Kuma kuji da kanku abinda yace.Comments