Main menu

Pages

MAKUDAN KUDADEN DA ATIKU YA DAMKAWA NAZIR SARKIN WAKA

 


Dalolin da Atiku Abubakar ya ba sarkin Waka Nazir


Kamar dai yadda muka samu labarin cewa ana yin primary election, Naziru na jin cewa Atiku Abubakar ya ci wannan primary to shikenan fa sai yayi tattaki har gidan Atiku Abubakar.Inda yaje yayi masa wata Waka, da ya ke cewa Atiku Abubakar shine Shugaban kasar da zai gyara Nigeria, da sauran yabo da banbadanci. Inda shi Kuma Atiku Abubakar ya dako wasu makudan kudade a Farar Leda wadda a cikin wadannan kudin gaba daya babu Nairan Nigeria duk dalolin America neya damkasu ga Nazir Sarkin Waka.To mudai a nan gaskiya wadannan mawaka basa ma kasarsu da yankindu adalci, su kansu kawai suka sani. Bai yuwuwa ka tsaya bon ra'ayin wani mawaki kamar yadda Naziru da Rarara kowa yake ma Dan takara shi campaign. Su sunje an shaka masu kudi Kai kana nan gefe na tiwo ma Wani gagaransa yake but ku ce Wani mawakine zai zaba maku abinda yafi. Haka kawai suje su kaimu su baro mu kamar yadda akayi a zaben 2015 da 2019. Gashi har gobe sai bakar azaba ake Tasha su kuwa mawakan Basu ma San ana matsalan kudi ba.To da shi Nazir da aka cika ma aljihu da kudi da katuwar mota, da Rarara da ya gallabi mutane da wakar Tunubu, duk ba Wanda zamu bi ra'ayin sa. Wannan zaben na 2023 mu dage da addu'ar samun shugabanni nagari, kar muyi sakacin da mukai a baya.


Ga Video kyautar da Atiku Abubakar ya yi ma Naziru.Comments