Main menu

Pages

KO KINSAN WANNAN BIRNIN DA SUKE KUKAN WUTAR NEPA TA MASU YAWA

 


Mazauna birnin da ke kukan wutar lantarki ta musu yawa


Garuruwa da birane da ke kusa da tafkin Geneva, babban birnin Switzerland sun kasance cikin duhu a wani mataki na fadakarwa da wayar da kan jama'a a kan muhimmancin sanin illar hasken fitulun lantarki.



An karkashe fitulun kan titi, sannan kuma aka shawarci mutane su ma su kashe kwayayen lantarki na gidajensu a lokacin.



Wadanda suka shirya wannan abu sun ce sakamakon ya kasance na mai ban sha'awa, yadda birnin ya kasance da duhu, a lokacin samaniya kuma ta kasance tarwal da ado na taurarin subahana, abin ba magana.



Daman tun ba yanzu ba 'yan sama jannati a birnin na Geneva sun sha kokawa cewa ba sa iya hangen taurari a sararin samaniya saboda fitilun kan hanya da suka mamaye titunan kasar



Masana a bangaren muhalli sun ce illar hasken wutar lantarkin na shafar dabbobi da shuke-shuke.



An bukaci mutanen kasar miliyan guda da ke zaune kusa da tafkin na Geneva da su saki jikinsu da wannan duhun da suka kasance a cikinsa a daren domin su ganewa idanuwansu yadda yanayin taurari ya ke da daddare a sararin samaniya.



Sai dai saboda dalilai na tsaro, ba a jefa birnin na Geneva gaba daya cikin duhun ba, sannan an bukaci masu tafiya a kafa da masu tafiya a kekuna da su sanya kayan da za a iya ganinsu a hanya don gudun kada a kade su da abin hawa ko su yi karo da juna.

Comments