Main menu

Pages

SABUWAR NA'URAN DA ZATA DINGA YIWA MATA RENON CIKI.

 



Sabuwar Na'uran da zata dinga raining ciki da haihuwa.


A 'ƴan kwanakin da suka gabata ne wani saƙo ya dinga yaɗuwa a shafukan sada zumunta da muhawara a Najeriya, mai taken "Haihuwa ba tare da renon ciki ba."


Saƙon, wanda aka fi yaɗa shi a zaurukan wassof wato Whatsapp groups, mai tafe da wani hoto na cewa:


"Sabuwar fasaha ce wannan wadda mata za su daina wahalar daukar ciki na tsawon watanni tara, da zarar an hada ƙwayoyin halittar namiji da ƙwan mace za a saka domin samar da ciki, sannan za a saka cikin wannan na'urar.


"Na'urar tun tana matakin farko a saka ta anan a ajiye sai bayan watanni tara (9) a kira uwa ta zo ta ɗauki ɗanta."Ya kuke kallon wannan fasahar?"



Sannan kuma saƙon yana tafe da wani hoto da ke ikirarin cewa hoton na'urar ce.

Ga alama mutane da dama da suka ga saƙon kai-tsaye sun yarda da shi ba tare da zurfafa bincike ba, kuma an yi ta tafka muhawara da nuna al'ajabi kan lamarin.


Akwai batun fasahar mahaifa amma kuma an sassauya zancen da bayanan yadda take aiki. Bayani zai zo a can ƙasa.


Irin muhawarar da aka dinga yi a kan saƙon

A bin diddigin da aka yi a wasu zauruka na Whatsapp, an ga yadda mutane suka yi ta bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin musamman ma mata.


An tsakuro wasu daga cikin saƙonnin a wasu zaurukan amma an ɓoye sunayen masu tsokacin kamar yadda suka buƙata.


1. 🤐 Ban san ma me zan ce ba wallahi


2. Ikon Allah. Kamar rayuwa Aliens


3. Shaƙuwa tsakanin iyaye da jariransu za ta ƙare kenan. Wannan abu dai bai yi ba a nawa ganin, duk da sauki aka samu.


4. Gaskiya bai yi ba. Ni ma na yi tunanin shaƙuwar nan. Wannan ɗaukar cikin na wata tara ba abin banza ba ne ba fa, yana da muhimmanci sosai.


5. Ban sani ba amma gaskiya ba na tsammanin wannan abin zai samar da ɗa lafiyayye, ko a farko ko a ƙarshe sai an ga illarsa a jikin yaron da aka haifa. Haba! Allah kadai ya san me ya tanada da yake zama har wata tara a ciki fa!


6. Ai kuwa za a ƙyanƙyashe Alien 😄


7. Na kasa gane kan wannan gudun ɗawainiyar da ake yanzu. A matsayin uwa kin guji ɗaukar ɗanki a ciki, ta yaya kike tsammanin yaron zai zama mutum mai ɗaukar nauyin kansa a rayuwa kuma iyayen ya tausaya muku? Allah kara kare mana imaninmu. Ya zamto jagoranmu.


8. Hmm kurum su hutar da kowa su yi kantin sayar da jarirai ka shiga ka zaɓi wanda ya yi maka.


9. Kuma har a zo suna a rinka cewa Allah yasa masu jinkai ne ko?


10. Ni kuma nawa tunanin kamar an yi ne saboda masu matsalar rashin haihuwa amma anazaune kalau me za ja maka wannan fitinar


11. Ga wanda ba zai iya haihuwa ba wannan ai lalura ce koni ce idan ba zan haihuwa zan yi dan na samu dan kaina.



Mece ce ainihin fasahar mahaifar?

A shekarar 2019 ne masana kimiyya a ƙasar Netherlands suka ce suna cikin shekara ta 10 ta samar da mahaifar roba wacce za ta iya ceto rayukan jarirai bakwai ko ƴan tayi.


Kafin nan, a shekerar 2017 likitocin fiɗa na yara a Asibitin Yara na Philadelphia a Amurka sun bayyana cewa wannan sabuwar fasaha za ta haɗa da saka ɗan tayi a cikin wata jaka babba mai kama da balam-balam mai ɗauke da ruwan mahaifa.


A lokacin sun ce sun gwada na'urar a kan ƴan tayin tumaki, inda suka haɗa cibiyar dabbar da wata na'ura mai musayar iskar gas a wajen waccar na'urar don taimaka wa jini ya ci gaba da samun iskar oksijin da abubuwan gina jiki.



An fara gwajin wannan mahaifar roba da ɗan tayin tinkiya

An ajiye wasu daga cikin jariran tumakin har zuwa lokacin da suka isa haihuwa, don haka idan har tawagar za ta yi nasarar samar da fasaha mai aminci haka, to mai yiwuwa su iya amfani da ita don ceto rayuwar jariran ƴan adam.


Kamar yadda aka sani ne a faɗin duniya haifar bakwaini na daga cikin manyan abubuwan da ke jawo mutuwar jarirai.


Amma wannan ci gaban fasaha ya kuma jawo tambayoyi a kan yadda za a dinga samar da jarirai a nan gaba a duniya.


Masu bincike na fatan mahaifar robar za ta inganta damar rayuwar bakwaini ko ƴan tayi, inda jariran za su ci gaba da girma tamkar dai suna cikin mahaifiyarsu.


Kenan batun wancan saƙon na sama da ke cewa ana dasa ƙwayayen haihuwar mace da namiji ne tun farko a cikin mahaifar robar ba haka yake ba.


Bayanan masana kimiyya sun nuna sai ɗan ya fara girma a cikin uwa sannan za a mayar da shi mahaifar robar idan an gano wata matsala da ka iya sa wa a rasa shi.


Lisa Mandemaker, ɗaya daga cikin waɗanda suka tsara aikin wacce take aiki da Cibiyar Lafiya ta Maxima don ƙirƙirrar mahaifar robar, ta ce idan aka ajiye jaririn a ciki sai a bar shi ya ci gaba da girma har sai lokacin haihuwarsa ya zo sai a fitar da shi.


"A lokacin da nake horo a fannin ƙwarewa a kan abubuwan da suka shafi lafiyar mata shekara 27 da suka gabata, na san yin irin wannan kimiyyar abu ne mai yiwuwa," a cewar Dr Guid Oei na Cibiyar Lafiya ta Maxima.


Ƙwararren ya ce babban bambancin da ke tsakanin wannan mahaifa ta roba da kwalbar da aka saba sa jariri bakwaini ita ce, "ita wannan mahaifar roba cike take da ruwa yayin da kwalbar sa bakwaini ke cike da iska.


"Kwalbar saka bakwaini waje ne mai haɗari ga jariran. Iska kan lalata huhu. Yayin da a cikin mahaifar roba kuwa an yi ƙoƙarin samar da duk wasu sinadarai na abinci da ruwan mahaifa da iska da jinin da jairi ke buƙata don ci gaba da girma," a cewar likitan.



Mene ne ba daidai ba a labarin da ake yaɗawa kan batun a Najeriya?

Ga alamu dai kamar yadda na faɗa a can sama, mutane ba su fahimci yadda wannan fasaha ke aiki ba, shi ya sa aka dinga yaɗa da labarin da cewa an ƙirƙire ta ne don samar da sauƙi ga masu gudun ɗawainiyar ciki.


Amma dukkan bayanan da masana kimiyya suka yi sun nuna cewa ita wannan fasaha ba a yi ta don hutar da ɗaukar ɗawainiyar ciki ba, an yi ta ne don rage yawan rasa jarirai bakwaini da ake yi da kuma rage yawan ɓarin ciki da wasu matan ke fama da shi, ta yadda za a ciro ɗan tayin a wasu makonni a saka shi a mahaifar robar don ci gaba da girma har ya isa lokacin haihuwa.


Wato kenan ita wannan sabuwar fasaha ta mahaifar roba za ta maye gurbin kwalbar adana bakwaini da aka fi amfani da ita, wacce suka ce ta fi haɗari ga jariran.


Sannan kuma hoton da ake yaɗawa tare da saƙon ba shi ne ainihin hoton mahaifar robar ba. Shi wannan hoto ma idan aka duba da kyau za a ga cewa zana shi aka yi, kuma ya fi kama da kwalbar sa bakwaini.


Ita sabuwar fasahar mahaifar robar tamkar balam-balam take.


Me jariri ke samu daga wajen uwa?

Miliyoyin shekarun da aka shafe ana samun juyin halittar ɗan adam ya sa ɗaukar cikin ɗan adam ya zama na daban wajen rikitarwa sannan kuma an samu ci gaba mai yawa a tsarin.


Mabiya ita ce abar da ta haɗa uwa da ɗan tayinta - ɗan tayin ne ke sa mabiya tana girma a jikin mahaifar uwa.


Iskar oksijin da sinadaran abinci na gina jiki da sinadaran hormone na shiga jikin ɗan tayin daga jikin uwa ta hanyar mabiya, abin da ke sa ciki ke bunƙasa har jaririn ya dinga girma.


Sannan a hannu guda kuma jaririn yana mayar da iskar da yake fitarwa ta carbon dioxide da sauran gurɓatattun abubuwa zuwa cikin magunar jinin uwar. Sannan zafin jikin uwa ma na da muhimmanci wajen bunƙasar jariri. Don haka mahaifar roba tana buƙatar kwaiwayon dukkan irin waɗannan abubuwan.



Waɗanne manyan tarnaƙi mahaifar roba ke da su?

Mai yiwuwa matakin da ba a fahimce shi sosai ba a ɗaukar ciki - kuma wanda ke buƙatar taka tsantsan - shi ne kusan kwana 10 bayan ƙwayayen mace sun ƙyanƙyashe, a yayin da ƙwaiƙwayen da ke haɓaka ke shigewa cikin mahaifar su fara girma.


A yanzu masu bincike suna gwada hakan ta ƙoƙarin tattalin ƙwayayen halittar mahaifa a wajen jiki, wanda a nan gaba za a iya kula da shi a mahaifar roba tare da samar wani waje da ɗan tayin zai girma.


Ita ma wannan tsokar mahaifar za ta buƙaci samun magudanar jininta - wani abu da har yanzu ba a samar ba.


Masana kimiyyar sun yi amanna cewa magance wannan lamari zai zama gagarumin mataki na gaba wajen samar da mahaifar roba.


Sannan a al'amarin ita wannan mahaifar roba akwai barazanar kamuwa da ƙwayoyin cuta, duk da cewa balam-balam ɗin da za a sa ɗan tayin an tsaftace ta da magunguna tare da rufe ta ruf.


Sannan kuma samun nau'ukan sinadaran abincin da sinadaran hormones ɗin da za su taimaka wa jaririn ma na iya zama ƙalubale.


A yanzu dai ko da a ce za a ci gaba da aikin, babu tabbas kan yadda iyaye za su ji dangane da hakan.



Comments