Main menu

Pages

ABINDA YA KAMATA KAYI IDAN SCREEN WAYARKA YA DAUKE.

 



Yanda zaka gyara phone screen din wayarka idan ya nuna farin labule

Duk yadda wayar ka takai da tsada ko quality, to kasani machine ce dai, Kuma duk wani machine dabi'ar sa shine na rashin yin aikin da ya dace wani lokacin koma ya tsaya gaba daya.




Don haka kuwa ashe abune Mai sauki idan lokaci guda kaga wayarka ta daina respond tayi hooking, Wani lokacin kaga ta koma blank bata nuna komai, (Hausa sukance farin labule) alhalin Kuma ba faduwa kasa tayi ba ko fafawa Ruwa.




Don haka abune mai muhimmanci kasan abinda ya kamata kayi idan hakan ya faru.



Akwai wani da ake cema Whistler, yayi magana da engineers biyu na waya Mr Joseph a GSM Village da Kuma Mr. Peter a Banex Plaza, don suyi bayanin abinda ya kamata mutum yayi idan wayarsa ta nuna farin labule.


A yadda sukace, ga hanyoyin da mutum ya kamata ya in don gyara wayarsa.;



Da farko sukace zaka danna power bottum da Kuma volume Amma wajen ragewan zaka danna ba karawan ba (long press) ma'ana ka danna ka rike kamar dai zaka kunna waya, zaka danne su na wasu 'yan mintuna. 




Daga nan wayar zata nuna tayi restart, sai kasa accept, bayan wasu 'yan mintuna, wayar zata dawo a kunne.




Idan kayi hakan but bata dawo ba, to wayarka na bukatar taga engineer din ya duba battery da screen clip. Shi screen clip shine yake rike da screendin wayarka, din haka idan yayi loose ma'ana yadan saki to doke screen zai koma blank.



Idan wannan Shima bai yi aiki ba to fa matsalar ta factory din wayar ne.



Idan Kuma iPhones 8 Zuwa abinda yayi kasa ne Wanda su suna da home buttons, zaka danna ka rike power buttons na tsawon seconds 8 to 10, don tayi restart. Ga iPhones X Zuwa sama Kuma suma zakayi pressing power da volume na kasa Shima na 8 to 10 seconds itama don tayi restart, Amma hakan zai yi aikine idan phone screen din na a on kawai baya responding ne. 



To Shima idan bai yiba to ya zama dole sai an Kai gyara kenan

Comments