Main menu

Pages

YANDA ZAKA TURA DM (DIRECT MESSAGE) A TWITTER GA WANDA KAKE SON TURA MAWA.

 


Yadda zaka tura Sako a Twitter


Idan zaka tura sako na DM ko private chat a Twitter shine, za kai amfani da wannan icon din Mai kama da envelope, a app na Twitter ko website.



Dms da private chat ne da zaka iya tura ma mutum daya ko fiye a Twitter. Sai dai kafin ka iya tura ma mutum sako ta private dole ne sai kayi following dinshi.



To shidai DM chat ne na private zakuyi firanku ba tare da kowa ya gani a cikin Twitter din ba kamar dai yadda zakai chat da mutum a Facebook.



Duk da dai a Twitter ba kowane zaka iya tura ma sako direct ba, sannan duk wanda yayi blocking dinka baza ka iya tura mai Sako ba har sai ya cire ka a block din. Yadda zaka tura sako a Twitter


1. Zaka bude Twitter a website browser.

2. Sai Kai clicking message icon din nan na wajen navigation din nan na browser daga gefen hagu.

3. Sai kayi click new message.


Bayan ka danna message icon, sai ka rubuta sakon da Zaka rubuta, idan kuma kana son Kara tura Wani sabon salon wannan message icon din dai zaka kara dannawa.


4. Idan zaka nemo Wanda zaka turawa sai ka rubuta sunan Wanda zaka turawa ta searching sunanshi. Idan sunan ya bayyana, sai ka danna sunan ka tura. Idan kana son turawa a group ne Kuma, Shima dai searching din zakai idan ya bayyana sai ka tura.


5 Bayan ka jera duk mutanen da kake son turawa sakon sai ka danna Next


6. Daga can kasan page din, zaka rubuta wani message din ta hanyar danna icon dake gefen hagu inda ake fara sabon rubutu.

7. Idan kana son saka photo a sakon sai Kai tapping a kan icon dake hagu da sakon sai kadda Kai dora photo ko photo Mai motsi(GIF)

8. Idan ka gama sai ka danna wannan arrow icon din na tura sako ka tura.


Ko da ace ka rubuta draft message, idan ka tashi turawa hakan dai zakayi.

Comments