Main menu

Pages

YANDA ZAKA GANE WANDA YA KIRA KA LOKACIN DA WAYAR KA TAKE A KASHE.

 Yadda zaka ga Wanda ya Kiraka lokacin da wayar ka take a kashe


Yanda zaka gane wanda ya kira ka lokacin da wayarka take a kashe ga dukkan network service da muke dasu to ga yanda za kayi.Kasancewar mutum zai iya kashe waya a lokacin da zai shiga Masalllaci ko wajen aiki misali an shiga meeting ko Kuma Mai gaba daya ta dauke saboda rashin caji, Ashe kuwa idan haka ta faru zaka so ka San waye ya kiraka lokacin da wayar take a kashe.A wannan posting za a nuna maka hanyoyin da Zaka bi don saita missed calls notification a SIM dinka din ganin Wanda ya kira wayarka a rufe ko ta dauke. Dukkan network din da muke dasu sun tsara mana yadda zamuyi muga Wanda ya kira lokacin wayar na rufe.Ga MTN suna Kiran tsarin da "MTN Missed Call Notification", su Kuma 9mobile suna Kiran shi da "Missed Call Notification", sai Airtel da Glo su Kuma suna cewa "Missed Call Alert".Yadda Za Ka Gane Wanda ya Kiraka

Lokacin da wayar ka take a kashe (MTN, 9mobile, Airtel, Glo).

A kasa ga cikakken bayanin yadda zakai subscribing wannan tsari, a MTN, 9moblie da Airtel.Yadda zaka kayi activating MTN Missed Call Notification shine;

Zakayi text ka rubuta SET 01 ka tura ma 100. Da ka tura to shikenan ka shiga tsarin Kuma kyauta ne.


Idan Kuma kana so ka fita daga tsarin wato deactivate to ga yadda zakayi.

Zaka tura sako ka rubuta SET 02 ka tura ma 100, shikenan ka fita daga tsarin.

Wannan shine yadda zakayi ka shiga wannan tsarin ga masu laying MTN. Da yadda zakayi Kuma ka fita.Ga 9mobile Kuma shine, zakayi dialling*229*269*1# da ka danna zasu turo ma da message cewa ka shiga tsarin ko Kuma ka tura sako ka rubuta MCNON ga 269 shikenan kayi activate 


Idan Kuma kana so ka fita daga tsarin sai ka danna *229*268*2# sai ka danna, daga nan zasu turo ma message cewa kayi deactivating wato ka fita daga tsarin, sai ka rubuta Sako da MCNOFF ka tura ma 269 shikenan ka fita.Sai Airtel shi kuna yadda akeyi shine, zaka danna *321 *881#, ko Kuma ka tura sako da START Zuwa ga 121 shikenan ka shiga tsarin.


Idan zaka fita sai ka danna *321 *883# shikenan ka fita daga tsarin.Sai Kuma tsarin Glo shi Kuma don sanin status din da kake sai Kai text da STATUS, zuwa ga 606, sannan sai Kuma ka karayin text da START M Zuwa ga 606, idan Kuma kana so kayi deactivating wato ka fita daga tsarin sai ka tura sakon STOP M Zuwa ga 606.


Ta hanyar bin wannan tsare tsare zaka san wanda ya Kiraka lokacin da wayar ka take a kashe. Ga Airtel idan ka kunna wayar ka zaka ga text da numbers din da suka kira ka, sannan Shima Wanda ya kira za a tura mai text cewa yanzu wayarka a kunne take.

Comments