Main menu

Pages

TSALLAKE RIJIYA DA BAYA, FASINJA YA SAUKE JIRGI DA KYAR SBD SUMAR MATUKIN JIRGIN

 Ma'aikacin kula da tashi da saukar jirage Robert Morgan ne ya taimaka wa Darren Harrison wajen saukar da jirgi


Wani fasinja da bai san yadda ake tuƙin jirgi ba ya saukar da wani jirgi a Florida na Amurka bayan matuƙin jirgin ya suma.


Cikin wani sautin murya daga cikin jirgin, ana iya jin fasinja Darren Harrison na faɗa wa masu kula da saukar jirgi cewa "an samu gagarumar matsala".


Wani mai kula da tashi da saukar jirage da ke koyar da matuƙa jirgi sabbi hannu ne ya taimaka wa mutumin yadda zai saukar da jirgin a filin jirgi na Beach International Airport ranar Talata.


Mutanen sun gamu a kakan titin jirgin daga baya don taya juna barka.


Ba a bayyana halin da matuƙin jirgin yake ciki ba, amma ana ci gaba da kula da shi a asibiti.


Tinja-tinjar da ta faru tsakanin fasinjan da mai taimaka masa ta haddasa dirama.


HARRISON: "Na samu gagarumar matsala a nan. Matuƙina ya ɗauke wuta. Ban san yadda zan tuƙa jirgin ba."


Mai Kula da Jirgi: "ATC: 333 Lima Delta, Roger, kuna ina yanzu?"


HARRISON: "Ban san komai ba. Ina iya ganin kogin Florida a gabana amma dai ban sani ba."


Mai Kula da Jirgi: "Ka bar fuka-fukai yadda suke kuma ka ci gaba da bin kogin, arewa ko kudu. Muna ƙoƙarin gano inda kake."


Robert Morgan, mai kula da tashin jirage a filin jirgi na Palm Beach International Airport, na cikin lokacin hutunsa lokacin da abokin aikinsa ya faɗa masa halin da ake ciki.


Mista Morgan bai taɓa tuƙa irin jirgin ba - Cessna 208 mai inji ɗaya - duk da shekara 20 da ya shafe yana aiki, amma ya yi amfani da taswirar masarrafar jirgin don ya taimaka wa mutumin saukar da shi.


"Na san cewa jirgin na tafiya kamar kowane jirgi. Na san cewa kawai dai akwai buƙatar na kwantar masa da hankali, na nuna masa hanyar kuma na faɗa masa yadda zai rage ƙarfin gudu don ya sauka," Mista Morgan ya faɗa wa WPBF-TV.


The plane and emergency crews


A sautin da aka naɗa, an ji Mista Morgan na koya wa mutumin "tura hannun giya gaba ka sauka a hankali sosai" lokacin da ya kusa sauka.


Bayan jirgin ya sauka, an ji Mista Morgan na yabon fasinjan a wajen sauran matuƙa jirgi.


"Ka ce fasinjojin sun sauke jirgin?" a cewar matuƙin jirgin. "Wayyo Allahna. Aiki ya yi kyau."


Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama na bincike kan lamarin.Comments