Main menu

Pages

PASSWORD DIN DA BAI KMT KAYI AMFANI DASU A SOCIAL MEDIA ACCOUNT DIN KA BA

 




Idan kana amfani da irin Wannan password din a social media accounts dinka to kayi maza ka canza.


Ire - iren password da za ayi saurin sace Maka information dinka na socal midia dinka.


Saboda kowa ya sani cewa password shine kadai matakin tsaro da muke amfani da shi wajen kiyaye online accounts dinmu. Dan haka ya kamata a ringa sanya su dai dai Kuma abinda kasan ba zaka manta ba, don gudun matsala.



To yanzu wadanne kalan password mafi hadari wajen amfani dasu, wanda wasu zasu iya accessing account dinka cikin sauki?


To a yau zamuyi magana ne akan wadannan password don a kiyayesu.



A duk lokacin da ka kirkiri password don kare Facebook, Twitter, Email, ko wani forum wanda kayi register akan duk Wani online accounts, to ya kamata ka kirkireshi da dukkan marakan tsaro ya zama strong password.




But wasu da dama suna kuskure wajen kirkiran common password, wadanda basu da karfi Kuma kowa zai iya kwatanta accessing duk Wani account dake da irin Wannan password. Password din dai sune kamar haka;



Generic keys, wato gama - garin lambobi wadanda ke da sauki wajen tunawa misali kamar "1234567", 1122334455, a kalmomi Kuma kamar "Like, da 'Yes", Kuma a yanzu kusan sune ma aka Fi amfani dasu ko da a ATM pin ne misalin "1234". Wannan Kuma babban kuskure ne yin haka, balle duba da yadda rayuwar yanzu take Kara yin tsada da tabarbarewar imani da tsoron Allah. Don haka sai a kiyaye.



Ku sani cewa yanzu masu attacking accounts da ire iren wadannan lambobi suke amfani Kuma sai suyi attacking duk Wanda yake amfani da irin Wannan password.



Don haka idan za kayi creating password to kar kayi amfani da common and simple or easy words ko numbers, kayi kokari kaga ka kirkiri dogon password at least 8 to 10 character, tare da symbols Wanda zai yi wahala ayi tunanin hadasu balle ayi samu damar Maka kutse a cikin accounts dinka. Allah Ya tsare mu da tsarewarSa Ameen.

Comments