Main menu

Pages

GOODLUCK JONATHAN YAYI FATALI DA FORM DIN APC DA AKA SAI MASA NA TAKARAR SHUGABAN KASA

 


Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya yi watsi da fom din tsayawa takarar shugaban kasa da aka siya ma sa ba tare da tuntubarsa ba.


A ranar Litinin 9 ga watan Mayun 2022 ne wata kungiya mai suna "Fulani Group" ta sayawa tsohon shugaban fom din takarar a karkashin jam'iyyar APC mai mulki wadda ta kada shi a zaben da aka yi a shekarar 2015, bayan shafe shekaru biyar ya na mulkin kasar.


Ƙungiyar magoya bayan Jonathan din ce ta yi karo-karo tare da saya wa tsohon shugaban fom din.


Sai dai sanarwar da mai magana da yawun Mista Jonathan ya fitar, ya ce ''ba mu da masaniya, ba kuma a tuntube mu ba kafin yanke hukuncin sayan fom din.''


Muna son shaidawa mutane cewa idan tsohon shugabankasa na son tsayawa takarar, zai sanar da al'umma, ba zai yi danwaken zagaye ba," in ji sanarwar.


A cikin wannan watan ake sa ran jam'iyyun siyasar Najeriyar za su yi zabukan fitar da gwani kamar yadda hukumar zaben kasar INEC ta shardanta musu yi kafin 3 ga watan Yuni mai kamawa, domin tsayar da 'yan takarar da za su fafata a zaben da ke tafe na shekarar 2023.Farashin fom din tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC mai mulki dai naira na gugar naira har miliyan 100 ne.


Duk wanda ya samu damar sayan fom karkashin jam'iyyar APC, zai fafata ne da dan takarar jam'iyyar hamayya ta PDP.


'Yan takarar jam'iyyar PDP kamar su Peter Obi, da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, sun kasance fitattu da suka nuna sha'awar takarar shugabancin kasar a PDP.

Comments