Main menu

Pages

ABUBUWAN DA AMARYA GOBE YA KAMATA TAYI KAFIN BIKI (4)



Ana So Amaryan gobe ta kula da Tsafta


Ana son amaryar gobe ta fara wannan shirin tun ana bikinta saura watanni uku.


Gaskiya qazanta ya kai qazanta a ce namiji ko mace basa rage gashin jikin su, saboda al’aura wuri ne da ya ke fitar da abubuwa da yawa musamman ga mace.


Kada ki rinka cutar da mijin ki kina qin tsaftace jikin ki. Haka nan kai ma kada ka rinqa cutar da iyalinka saboda tsafta da kwalliya suna da mutukar muhimmanci ga ďan adam.


Rayuwar Manzon Allah (SAW) shine mafi kyawun rayuwa ya koyar da musulmai dukkanin kyawawan dabi’u. Tsarki da tsafta suna da babban matsayi a addinin musulunci wannan ne ma har yasa Annabi (SAW) yace:

"Tsafta tana daga cikin imani"

Yana da kyau ko wane musulmi mace ko namiji su fahimci muhimmancin tsafta Kuma su rinka kasancewa cikin sa a koda yaushe. Nuna halin ko in kula yana jawo ma mutum cututtuka da rashin girma a wurin mutane, kuma zai sa mutane su yi nesa-nesa da shi saboda kada ya zo kusa da su su ji wani wari ko tsami na fitowa daga jikin sa. Zan tattaunawa Abubuwan tsafta da yanda za’ayi tsafta din dama shawarwari Idan mutum yana da kasala wurin wasu tsafta.


Farko zan fara ne da rage gashin wurare biyu na jikin mutum, wato hammata da kuma qasan sa, kamar yanda ya zo a hadisi Abu Hurairah ya ji Annabi (SAW) yana cewa:

“Ayyukan da’a guda 5 ne: “Kaciya, da cire gashin hammata, da rage gashin baki, da yanke farce, da tsige (cire) gashin mara.


HAMMATA DA QASAN MUTUM

Wannan wuraren biyu suna da mutukar bukatar kulawa, saboda wurare ne da ba su da wuyan sun fara fitar da wari, domin su kullum a lullube suke. Don haka ne Manzon Allah (SAW) Ya umurci mutane da kar su wuce kwana 40 ba tare da sun rage gashin wurin ba. Sannan ba dole sai 40days ba saboda akwai masu kufan gashi da kafin ma 40days gashi ya fito musu sosai.


Don haka sai a kuka da tsaftace wannan wuraran, sannan Amarya ta kula sosai da tsaftar muhalli, bayan tsaftar jiki to sai ta muhalli aga ko Ina naki fez fes ba qazanta. Saboda duk yadda Zaki gyara jikinki Amma muhalli da datti to, akwai kura, don baki cika Mai tsabta ba.

Idan kin karanta ki turama wasu suma su amfana. 

Comments