Main menu

Pages

 



KALOLIN YADDA AKE GURASA

A wannan bangaren zamu kawo maku yadda aleyin gurasa kala daban daban Insha Allah. 

GURASAR TANDERU

Kayan da za a buqata.

1. Fulawa

2. Yis

3. Kantu/ridi(optional)

4. Sikari 

5. gishiri

YADDA ZA KI YI

Ki sami fulawarki ki tankade ki zuba mata yis, ki zuba ruwa ki kwaba, ka da ki kwaba shi da ruwa, ki kwaba shi da dan tauri. Idan kina son Gurasa mai sikari, sai ki zuba sikari a cikin kwabin , idan kuma kina son mai gishiri ne, sai ki zuba gishiri a cikin kwabin. Idan lokacin zafi ne za ta yi saurin tashi saboda dama yis zafi yake so ,awa uku zuwa hudu ya ishe shi ya tashi.



 Amma idan lokacin sanyi ne yakan dade bai tashi ba. Idan kina so ki yi Gurasa da safe, to sai kin kwaba fulawarki tun da daddare, kuma ki nemi wuri mai dumi ki saka ki rufe sosai domin ya tashi. Idan kin tabbatar kwabinki ya tashi, sai ki zuba karare a cikin Tanderu, ki kunna wuta domin tanderun ya yi zafi, idan kin tabbatar tanderun ya yi zafi sosai kuma karan ya cinye sai ki yayyafa ruwan kanwa a ciki, ki saka tsintsiya ki share toka-tokar data makale a cikin tanderun. 



Sai ki kawo kwabinki ki cura shi ya yi fadi, ki fadada da hannu , yadda dai ki ke son fadinta ya kasance, idan kina son kantu/ridi sai ki zuba dan kadan a kan gurasar a tsakiya, idan kuma ba kya so shi kenan sai kawai ki saka curin da ki ka yi a cikin tanderun, idan kin gama sakawa sai ki kawo tire ki rufe tanderun. Ta kan dau kamar minti ashirin zuwa minti ashirn da biyar kafin tayi. Kai ba ma sai kin kalli agogo ba , da ta yi za ki ji kamshi ya turare ko ina a gidan . Sai ki kawo wuka da tire, ki ringa saka wuka kina bambarota tana fadawa kan tiren. Amma sai kin yi a hankali saboda zafi ka da ki kone domin tanderu yana da zafi sosai.



2- GURASAR TUKUNYAR KARFE

Kwabin gurasar dai duka daya ne. Abin da za ki yi a nan shi ne ki sami tukunyar karfenki mai kwari, ki dorata akan wuta, idan ta yi zafi sosai sai ki zare itatuwan ki bar garwashin, saboda ka da gurasar ta kone, sai ki cura gurasar ki fakadata ki saka cikin tukunyar, idan kin gama sai ki kawo murfi ki rufe. Idan ta yi zaki ji ta fara kamshi.



3-GURASAR TANDERUN NASARA (OVEN)

Kamar dai yadda na ce a sama, kwabin duka daya ne. Ki tabbatar kin kunna (oven) din ki ya yi zafi sosai, sai ki kawo tiren gashi ki shafa masa bota, sai ki kawo kwabin ki cura, ki kuma fadada, sai ki saka a cikin tiren gashi, idan kin saka duka ko kuma iya yadda zai dauka, sai ki mayar da tiren cikin (oven) din ki rufe. Zai dauki kamar minti goma sha biyar zuwa minti ashirin kafin ta yi. Ko kuma da kin fara jin kamshi to tayi , sai ki cire.


Kamar dai yadda na fada a sama ana iya cin gurasa da abubuwa da dama, sai abin da kika zaba za ki ci da ita. Amma duk a cikin wadannan hanyoyin yin gurasa duk ta cikin tanderu tafi dadi, domin tanderu tukunya ce wadda ake ginawa da kasa, kuma kowa ya san duk abin da aka yi shi a cikin tukunyar kasa kamshinsa daban yake. Saboda haka Uwargida idan za ki dage sai na ce ki gwada yin gurasa a cikin tanderu, amma ayi hankali da zafi , ka da a kone. Amma idan ba kya son wahala to sai kawai ki yi ta a cikin tanderun Nasara (oven) a saukake kenan.



4- BANDASHO

Bandasho shi ma dai da gurasa ake yi, kuma ba wani wahala ne da shi ba, ba ya daukan lokaci , kuma baya cin kudi. Saboda haka Maigida ban da korafi!

KAYAN DA ZA KI TANADA

1. Gurasa mai gishiri

2. Dakakken kuli-kuli

3. Albasa

4. Tumatir

5. Mai

YADDA ZA KI HADA

Ki sami gurasarki ki saka ta a cikin ruwan dumi, tayi kamar sakan biyar a ciki sai ki cire, ki tsanar da ita, ko kuma ki turarata, abin da dai ake so shi ne gurasar ta yi laushi sosai,sai ki zuba mai gaba da bayanta, sai ki kawo kuli-kuli ki barbada, shi ma gaba da baya, sai ki yanka tumatir da albasa akai, idan kina bukata kina iya kara mai domin ya ji. Ki tabbatar kuli-kulinki ya ji magi, ba sai kin zo kina karawa bandasho din ba.

To Uwargida a ci dadi lafiya! Ga gurasar Kanawa yau a Madafinki!

Comments