Main menu

Pages


        


HUMRA

Humra turare ne wanda aka samo asalinsa daga Arabs (Larabawa)

kuma Bare-bari suka dauka a matsayin kwaikwayon al’aadar.

sannan ta yadu a kasar Hausa, kusan duk mata sun karbe shi sakamakon irin ingancinsa tare da cikakken muhimmmancinsa.



Turaren Humra na dauke da sinadarai masu kamshi, ana kuma hada shi ne da saiwoyi da nau’oin turarruka daban-daban, kuma ta kan zo a nau’in bakar humra ko fara har ma da koriya.

Abubuwan da ake hada bakar Humra da su

▾ Ruwan turare (Alchohol) litre 1

▾ Madarar turare 1/6 litre

▾ Ambir 4 (gwayar shi)

▾ Garin sandal cb 2

▾ Garin Humra cb 3

▾ Garin soyayyen kaninfari ck1

▾ Mahalan (gari) ck 1/2

*Yadda ake hada bakar Humra:*

①. Za’a sami ruwan turare a zuba masa nikakken ambir

②. Sai a kawo garin nikakken tankadadden sandal da garin Humra da soyayyen garin kaninfari, da garin mahalan, a zuba a hada su a girgiza, a kawo madarar turare irin nau’in da ake bukata a zuba, zai iya kasancewa fiye da daya ko fiye idan sun hadu sai a zuba a cikin kwalbar turare a rufe.



Farar Humra da Koriya

Ita ba’a sa mata garin Humra, shi ne kadai babu, a cikin koriyar Humra kuma kala ake sa wa koriya, ita ma din kadan, kuma babu garin Humra a cikinsa.

Wannan kawai shi ne bambanci tsakaninsu

Comments