Main menu

Pages

MATAR DA TA NUNA TSANTSAR RASHIN IMANI GA MIJINTA




GA FUSKAR TA: Itace wacce ta kashe mijinta ta hanyar Burma Masa wuka a wuya...


Ga Cikakken labarin abin yadda ya faru...


Sunan ta Atika 'yar Asalinta wani kauye ce a karamar hukumar Daura ta Jihar katsina suna zaune da mijinta a garin Mararaban Abuja da jihar Nasarawa Haihuwarsu Hudu da mijinta amma 'daya ya rasu daga cikin 'ya 'yan su saura Uku yanzu, mijinta wanda ta kashe bakaniken mota ne sunan sa Ibrahim Ahmad.


Kusan watanni biyar da suka wuce ya Kara aure kusan Shekara kenan da yayi Sabon gida Suka koma. Atika ta kasance mai tsananin kishi suna yawan yin fada da mijinta, anyi mata shedar masifa sosai, kuma kafin Ibrahim ta fara yin wani aure, an ruwaito cewa shima tsohon mijinta na farko barazanar Kai farmaki take yawan yi masa da wuka hakan yasa ya rabu da ita, a baya ta ta6a yankan matar yayan mijinta da wuka a Lokacin da suke fa'da suna gida daya kafin mijinta yayi Sabon Gida su koma.



Ranar Asabar din da ta gabata da misalin karfe 08:00pm Ibrahim ya dawo gida Kai tsaye ya wuce 'dakinta domin Kai mata Golden Milk shigarsa ke da wuya sai rikici Ya barke tsakanin su lamarin da ya kai su ga har ta yanka masa Chico a hannu ta fasa hannun sa ta kuma yanka Masa Chizo a kirjinsa shine ya fito da sauri ya nufi wajen 'Daya matarsa yace da ita ta daure Masa hannun sa.


 Bayan an daure Masa hannun ya juya baya Yana tafiya ita Kuma ta sake fitowa ta zaro wuka ta biyoshi ta baya ba tare da sani ba ta Burma Masa a wuya tsakanin kafadarsa da wuyansa ta sake Chaka Masa a Gefen kirjinsa kusa da hammatarsa a Lokacin ne Ibraheem yace da Ita kin kasheni, Kamar yadda take shedawa da kanta.


A Lokacin ne Kishiyar ta tayi sauri ta shige dakinta ta rufo kofa ta kulle Kuma Bata fito ba sai da ta tabbatar mutane sun shigo gidan.


Ibraheem ya fara gudu zuwa bakin kofar gida GATE Yana Ihun Neman taimako amma Atika ta sake zaro wata katuwar GORA Sanda ta bishi da gudu ta Buga Masa a kansa ta Kuma Buga masa har sai da Kwakwalwarsa ta fito ya Kama kofar GATE hannunsa duk jini ga wuyan sa yana feshin JINI daga nan ya Fadi ita Kuma ta fara IHU tana cewa na Shiga Uku na kashe mijina da hannuna, an dauki Ibraheem zuwa asibitin kafin a Kai asibiti ya rasu, Innalillahi wa'innah Ilayhim Raj'un Allah ya jikansa da Rahama.


Yanzu haka dai an yiwa Ibraheem jana'iza kamar yadda Addinin islama ya tanazar ita kuma tana hannun rundunar 'yan sanda ana cigaba da bincike.


Go Hoton Atika makashiya.



Ga Hoton Ibraheem wanda aka kashe.



GA Hoton Kofar Shiga gidan GATE Wanda JINI ya lalata a Lokacin da Ibraheem ke kokarin fita domin neman dauki.



GA Hoton Babban 'dan su namiji na dauki Hoton ne a makabarta a Lokacin da ake kokarin birne malam Ibraheem mahaifinsa. Sai Kuma Hoton Sauran 'ya 'yan su mata yara mata Biyu.


Ya Allah Ka tsaremu da sharrin mata marasa Imani ka bamu mata masu Imani ka hanamu mu'amulla dasu ta kusa.


Ya Allah Kasa mu Fi qarfin zukatanmu. Ameen.

Comments