Main menu

Pages

AMFANIN MANGORO GA LAFIYAR JIKI


Amfanin Mangoro

Wato jama’a da dama sukan sha mangwaro ne kawai ba tare da sanin menene asalin amfaninsa ga jikkunansu ba, asali ma wannan shi yasa birai ke kaunar shan mangwaro.


Ba za’a ga laifin su idan aka yi duba ga zakin da mangwaro yake da shi, musamman idan mutum ya samu binta siga, ko yar kamaru ko kuma mai warin gawasa, kaga kuwa duk mutumin dake yin karo da irin wannan mangwaron  sai a barshi yasha son ransa.



Kamar yadda aka saba arewarmu ba tayi kasa a gwiwa ba, wajen shuka ko ince dasa Mangwaro. Ga wasu alfanun Mangwaro ga dan adam guda 6, kamar haka:


1- Maganin ciwon daji (Kansa)

Bincike da kwararru suka gudanar ya tabbatar da cewa mangwaro na dauke da sinadarai kamar su ‘quercetin, isoquercitrin, astragalin, fisetin da gallic acid’ wadanda suke maganin ciwon daji, musamman muggan ciwukan da suka shafi nono, mara da kuma sikila.



2- Rage kiba

Sakamakon kasancewar sinadarin ‘pectin da vitamin C’ a cikin mangwaro da kuma bawon mangwaron kansa, yasa mangwaro na hana mutum kiba ta hanyar narkar da kitse a jikin mutum.



3- Gyara fata

Idan kana so fatar ka tayi kyau, tana kyalli tana sheik, musamman ga yan mata, toh kid age da shan mangwaro, saboda sinadaran dake cikinta suna gyara fata tare da maganin kurajen fuska.



4- Kara lafiyan Ido

Masana sun tabbatar da kasantuwar sandarin ‘Vitamin A’ dake gyara ido a cikin mangwaro, don haka mangwaro na kara karfin gani, kuma yana maganin bushewar idanu.



5- Kara karfin garkuwar jiki

Yawan shan mangwaro na kara ma mutum karfin garkuwar jikinsa masu yakar cututtuka a jikinsa, ba komai ya sanya mangwaro zamantowa haka ba illa tarin sinadarin ‘Vitamin C’ dake a cikinsa.



6- Taimakawa wajen nika abinci

Mangwaro na dauke da wasu sinadari masu matukar muhimmanci dake taimakawa wajen nika duk abincin da mutum yaci, da wanke cikin kansa. Sanadiyyar haka mutum ba zai yi fama da rudewar ciki ba.


Comments