Main menu

Pages

SAUQIN NAQUDA, DA FITOWA. YARO CIKIN SAURI

 


SIRRIKA 4 GAME DA NAQUDA DA SAUQIN HAIHUWA:

RUBUTU GA MACE MAI NAQUDA:

Idan mace na shan wahala sosai wajan haihuwa, to daga ta soma naquda, a samu bawon ƙwai (kwanson ƙwai) da dama, sai a niqe shi ya yi laushi sosai, sai a Rubuta wannan aya “YAKHRUJU MIN BAINIS-SULƁI WATTARA’IB” qafa 41.

يخرج من بين الصلب والتراءب

Sai a wanke rubutun, sannan sai a zuba wancan garin bawon ƙwai a ruwan ɗumi a gauraya, sai kuma a zuba ruwan rubutun a ciki (ta yadda zai zamo ruwan yana da ɗumi sosai), sai a ba mai naqudar ta riqa sha. Insha Allah za ta haihu da kanta cikin sauqi, wannan Mujarrabi ne sosai!RUBUTU GA MACE MAI NAƘUDA:

An ruwaito cewa, idan haihuwa ta tsananta ga mace, to a rubuta mata surar ‘Inna’anzalnahu’ ta sha, wurin zai buɗe ɗan ya fito da izinin Allah. Haka nan ana son yawaita karanta ‘Inna’anzalnahu’ akan mace mai naquda. (Mujarrabatul Imamiyyah, 146).ADDU’O’I GA MACE MAI NAƘUDA:

-  Yayin da mace take fama da naƙudar haihuwa, in aka tofa Fatiha qafa Saba’in (70) a cikin ruwa mai tsafta aka ba ta ta sha, za ta haihu cikin sauqi da izinin Allah.-  Idan aka rubuta “Suratu Yaseen” aka bai wa mace ta sha, to nononta zai yawaita, wato jaririnta zai samu isasshen Nono mai inganci da izinin Allah.


Comments