Main menu

Pages

KO KUN SAN ILLOLIN DA SHAN RUWAN SANYI KE HAIFARWA?

 


MUHIMMANCIN AMFANI DA RUWAN DUMI GA MACE


Mafi yawan mata ba su damu da yin amfani da ruwan dumi ba, to lallai daga yau ki sani cewa ruwan dimi na da matukar mahimmanci ga jikinki. Ruwan dumi

yana kara wa mace lafiya a jikinta fiye da jikin da namiji. Idan da baki yin amfani da ruwan dumi a jikinki, to daga yau ki fara za ki sha mamakin yadda jikinki zai koma.Da wannan ne na ke jan hankalin ‘yan uwana mata da mu guji yawan amfani da ruwan sanyi, domin ruwan sanyi yana da illa. Ga kadan daga cikin illolin da ruwan sanyi ke haifarwa.


Tsaida Bugun Zuciya

Bugun zuciya shi ke gyara dumin jiki da dai-daita numfashi, to ruwan sanyi yana sa bugun zuciya ya rika raguwa har takai ga tsayawa. Ko kun san cewa yawancin ‘yan fim na kasar Indiya da ‘yan bal da ‘Boding’ da ‘Wrestling’ tsayawar bugun zuciya ke yin ajalinsu. Kuma bincike ya nuna yawancin shan ruwa mai sanyi ya yin da suke aiki ne yake jawo masu hakan.Lalata Tsarin Kayan Ciki:

Shan ruwan mai sanyi yana tattare hanta guri daya sai ya sanya abinci ya ki narkewa da wuri, hakan ke jawo matsalar hanji (Ulcer) ke nan ko kuma tashin zuciya. Yawan zub da yawu ko tashin zuciya ko kuma saurin kullewar ciki.Dauke Karfin Jiki

Duk da cewa shan ruwan sanyi kan sa mutum ya ji dadi, amma a hankali yana dauke masa karfin jiki sakamakon lokacin da ruwa mai sanyi ya shiga jikinsa dole sai na’urorin jikin sun yi kokarin ganin sun maida wannan ruwan ya dai-daita da dumin jikin, hakan yana sa su yi rauni sakamakon kokarin da suke yi yana wuce haddi. Ko kun lura duk sanda kuka sha ruwan sanyi sai kun ji duk jikinku sanyin ya ratsa kaman farkon zazzabi a hankali kuma sai ku ji ya daina.Ciwon Makogwaro Da Dakushewar Murya

Yawan amfani da ruwan sanyi yana lalata jijiyoyin makogwaro har su kai ga ba sa amfaninsu yadda ya kamata. Idan mutum ya kai shekaru 40 yana san ruwan sanyi sai ya fara fama da ciwon makogwaro da dakushewar murya ta fashe kwatankwacin mashayin taba.Ciwon Hanta Da Koda

Dukkan su suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu, don haka yayin da mutum ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi zai zamo su kuma suna cutuwa ta yanda aikinsu zai fara kasa, indan haka ta samu mutum ya shiga mastala.Busar Da Ruwan Jiki

Akwai na’urori a jikin Dan’adam da aikinsu shi ne, sadar da ruwa ko’ina na jikinsa zai samu damar motsawa cikin nishadi. To wadannan na’urori su kan yi sanyi sakamakon ruwan sanyi sai su zama jikin ba kwari.Matsalar Ma’aurata

Wannan abu ne tabbatacce har ga likitocin zamani cewa, shan ruwan sanyi yana raunata mazantakar namiji yana kuma busar wa mace in mahaifarta na da rauni yana iya hana haihuwa. Yana tsinka maniyyin namiji ya zama yana saurin biyan bukata ko kuma na rage masu kuzari. Yana dauke ni’imar jiki su zamo ba sa gamsuwa da juna.
Basir Da Ciwon Kai Na Gefe (Migraine)

Shan ruwan sanyi kamar yanda na ce muku, yana tattare hanji hakan yana kawo mutum ya kasa bayan gida sai ya hadu da basir. Sannan yana kawo ciwon barin kai wanda ake cewa ‘migraine’. Shi kuma ‘migraine’ yana kashe jijiyoyin jikin ido a ta yadda za a daina gani sosai, indan ma yayi nisa har hauka yana sawa.Amfanin Ruwan Dumi

 Sun Kasu Kamar Haka:~

 yana taimaka wa mace wajen kashe mata wasu kwayoyin cuta idan tana tsarki da shi. Yana kuma kara mata ni’ima a matsayinta na matar aure.


Ruwan dumi

yana zama kariya ga mace wurin kamuwa da cututtuka idan tana yin wanka da shi. yana kuma gyara wa mace fata ta yi kyalli ba tare da kin yi bilicin ba.


Ruwan dumi

 yana mikar da hanjin ciki lokacin da suka tattari sakamakon yunwa ko kuma an yi azumi. Ina bukatar idan mutum ya dade bai ci abinci ba, to idan ya zo zai ci ya fara da abu mai zafi domin ya mikar da hanjinsa kafin wani abincin da bai da zafi.


Ruwan dumi

 yana kara dankon zamantakewar aure, idan mace tana yin tsarki da ruwan dumi yana kara mata ni’ima ta yadda mijinta zai gamsu da ita.


Idan mutum yana shan ruwan sanyi yana kara wa na’urar jiki lafiya. Yana kara wa jikin karfi da walwala ta yadda kowani bangare yayi aiki yadda ya kamata.


Ruwan dumi

 yana kara karfin makwogoro, ta yadda muryar mutum zai fita kamar wajen karatu ko kuma wajen bayani ta yanda mutane za su fahimta.

Comments